Hukumar FCTA ta gargaɗi masu gudanar da sana’ar kanikanci a gefen hanyoyin jirgin ƙasa

Daga AMINA YUSUF ALI

Hukumar gudanar da al’amuran Birnin Tarayyar Abuja (FCTA), a ranar Lahadin da ta gabata ta yi jan kunne ga masu buɗe shagunan kanikanci a gefen hanyoyin jirgin ƙasa a Abuja.

Daraktan kula da cigaba na FCTA, Director Muktar Galadima, shi ya bayyana wannan gargaɗin. Kuma a cewar sa nan gaba hukumar za ta dinga kama waɗanda suka yi kunnen ƙashin a game da dokar tare da ƙwace ababen hawan da suke aikin a kai.

Galadima ya ƙara da cewa, waɗancan kanikawa za a gurfanar da su a gaban kotun tafi da gidanka. Sannan ya ƙara da cewa, da ma tun a baya hukumar ta sha gargaɗin makanikan gabaɗayansu a kan su tattara su koma unguwannin Apo da Wumba na Abuja don cigaba da sana’ar su.

A cewar sa, kanikawa da dama sun yi buris da wannan doka da umarni abinda sanadiyyar haka ya sa aka samu matsaloli da dama har ma da gurbata yanayi.

Galadima ya bayyana cewa, a yanzu haka dakarun hukumar wanda shi ne jagoransu a matsayinsa na darakta, za su dawo da aikinsu na rangaɗin wanda a da suka saba yi a ƙarshen kowanne mako domin su daƙile karya doka da laifuffuka da suka yawaita a birnin.

Hakazalika a cewar sa, dukkan wasu dazuzzuka ma da suke barazana ga tsaron ƙasar nan za a kawar da su. Domin a cewar sa, wasu dazuzzuka tuni suka zama maɓoyar ɓata-gari.

Hakazalika, wannan a cewar Daraktan yana daga dalilai da suka sa suka ƙara wa kansu ranakun aiki daga kwana biyar zuwa bakwai. Kuma sannan a cewar sa, su waɗannan wurare gwamnati ba ta mallaka wa kowa su ba. Amma kuma dole ne gwamnati ta kula da su.