‘Idon Mikiya’: Amnesty International ta yi tir da matakin NBC a kan Vision FM

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Amnesty International ta yi Allah-wadai da matakin dakatar da tashar Vision FM 92.1 Abuja, daga gabatar da shirin nan nata mai taken ‘Idon Mikiya’, da hukumar kula da kafafen yaɗa labarai ta ƙasa, NBC ta ɗauka.

Ƙungiyar ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta cire wa tashar rediyon takunkumin da ta ƙaƙana mata da kuma sake duba tarar da ta zabga mata.

Ƙungiyar ta yi waɗannan bayanan ne cikin wata sanarwa da ta fitar da ta sami sa hannun Daraktan ƙungiyar, Osai Ojigho, tana mai cewa ɗaukar matakin tamkar farmaki ne ga ‘yancin bayyana ra’ayi.

Ta ce dole ne NBC ta zama mai kiyaye doka da martaba harkokin ‘yan jarida don tattauna batutuwan da suka shafi al’umma.

Ta ƙara da cewa, yawa-yawan zabga wa gidajen rediyo tara, dakatar da shiryre-shiryensu da kuma rufe tashohin don sun gabatar da shiri kan abin da ya shafi al’umma, hakan ba zai haifar da ɗa mai ido ba wa ‘yancin ‘yan jarida a Nijeriya.

NBC ta ƙaƙaba wa Vision FM takunkumi ne tare da cin ta tara na miliyan 5 bisa samun ta da aikata abin da ta ce ya saɓa wa dokarta wanda kuma hakan illa ce ga sha’anin tsaron ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *