’Yan sanda sun mamaye sakatariyar APC yayin rantsar da shugabannin jihohi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Jami’an Rundunar ’Yan Sanda ta Nijeriya sun mamaye sakatariyar jam’iyyar APC ta ƙasa a Birnin Abuja.

Wannan dai na zuwa ne gabanin ƙaddamar da shugabannin jam’iyyar na jihohi da aka yi a jiya Alhamis. An tattaro daga majiya mai tushe cewa shugabannin jam’iyyar na ƙasa sun tura ’yan sanda domin daƙile taɓarɓarewar doka da oda. Sassan jam’iyyar APC da dama sun shiga cikin rikici biyo bayan sakamakon zaɓen da aka gudanar na jihohi a bara.

Jam’iyyar ta tsayar da ranar babban taronta na ƙasa:
Za a gudanar da babban taron jam’iyyar APC na ƙasa a ranar 26 ga watan Fabrairu kamar yadda aka tsara, jam’iyyar mai mulki ta tabbatar.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa da kwamitin riqo na jam’iyyar (CECPC) ya aike wa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (APC) domin cika wa’adin kwanaki 21 da hukumar zaɓe ta gindaya na gudanar da zaɓen.

An miƙa wasiƙar ne da safiyar Alhamis a hedikwatar hukumar zaɓen.

A ƙarshe dai ci gaban ya kawo ruguza jita-jita a kafafen yaɗa labarai cewa hukumar CECPC na shirin sauya ranar.

Yayin da ya rage kwanaki uku kacal da kundin tsarin mulkin ƙasar ya bayar, jam’iyyar APC mai mulki ta sanar da INEC aniyar ta na gudanar da babban taronta na ƙasa.

Dangane da sashe na 85 (1) na dokar zaɓe (2010) da aka yi wa kwaskwarima, an wajabta wa dukkan jam’iyyun siyasar ƙasar nan da su bai wa hukumar wa’adin aƙalla kwanaki 21 kafin gudanar da babban taro.

Bayan da aka yi ta ja-in-ja, bisa la’akari da rikice-rikicen da suka dabaibaye sassan jihohinta, wata wasiƙa ta fito a ranar Alhamis mai nuni da cewa jam’iyya mai mulki ta sanar da hukumar zaɓe taron da ke tafe. 

A cikin wasikar mai ɗauke da kwanan watan 2 ga Fabrairu, 2022, APC ta sanar da Hukumar INEC game da matakin da ta ɗauka na gudanar da babban taronta na ƙasa a ranar 26 ga Fabrairu.