Ina shinkafar Tinubu ta maƙale ne?

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Tun da Gwamnatin Tarayya ta bakin Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan ’Yan ƙasa Mohammed Idris, ta sanar da aikawa da tireloli 740 ga dukkan jihohin ƙasar nan har da Abuja, domin rabawa ga talakawa da ke rayuwa cikin ƙuncin talauci da yunwa, ‘yan Nijeriya ke ta zuba ido da tunanin ganin wannan tallafi ya isa gare su, musamman ganin cewa kowacce jiha ta samu kason tirela 20 maƙare da buhunan shinkafa. Yayin da aka bayyana cewa a kowacce tirela akwai buhu 1,200, sannan a kowanne buhu akwai shinkafa da nauyinta ya kai kilogram 25. 

Kamar yadda sanarwar ta bayyana, Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin lallai a tabbatar shinkafar nan ta isa ga kowanne lungu, kuma a ba da ita ga talakawa mafiya buƙata da ke lunguna da karkara, don ta rage musu raɗaɗin tsadar abinci da ake fuskanta a ƙasa. 

Idan za ku iya tunawa, wannan ba shi ne karon farko da gwamnatin Shugaba Tinubu take ba da irin wannan tallafi na kayan abinci ba. Ko da a shekarar da ta gabata ma a 2023, sai da gwamnatin ta sanar da warewa kowacce jiha Naira Biliyan 5 da tirelolin shinkafa 180 ga kowacce jiha, a matsayin tallafi, don rage raɗaɗin da cire tallafin man fetur ya haifar ga jama’a. 

Amma kamar yadda ta faru a wancan karon, rijiya ta ba da ruwa ne guga ta hana! Gwamnatin Tarayya tana iyaka nata ƙoƙarin don ganin ta taimaka wajen samar da sauƙi a rayuwar ’yan Nijeriya, amma wasu ’yan siyasa da baragurbin wasu gwamnoni, sai su hau kai su wawushe abin da yake rabon talakawa ne, su kai gidajensu da na magoya bayansu, su raba wa waɗanda suka ga dama, sauran jama’a kuma a raba musu mudu-mudu ko rabin mudu, su je su ciyar da iyalinsu. Abin takaici da ban haushi a wasu wuraren har warwaso ake sa talakawa su yi, wanda yake da ƙarfi ya ɗebi rabonsa, wai ba zai yiwu a bai wa kowa cikin tsari ba.

A wannan karon ma na lura irin haka ce ke shirin faruwa, don kuwa har yanzu tsit ka ke ji a wasu jihohi, babu labarin zuwan shinkafa ko kuma yaushe za a fara rabawa. A wasu wuraren kuma gwamnati ta sa ana ta raba shinkafar a ɓoye ana mayar da ita mudu biyu zuwa uku, a ƙananan buhuna, yayin da ake manna hoton gwamna, don ya nuna shi ne ya bayar ba shugaban ƙasa ba. A ganinsa hakan ne zai gyara siyasarsa. A wata jihar ma na ji cewa a maimakon a ba da shinkafar sai aka sayar aka raba wa wasu tsirarun mutane da Allah Ya ƙaddara da rabonsu Naira 1,500, a matsayin tallafi su je su yi cefane. Kuɗin da ba zai saya musu mudun shinkafa ’yar tsinta ba, sai dai sinƙin taliya ɗaya. Subhanallah! 

Nasan ba za ku kasa jin labarin inda jami’an tsaro a wasu jihohi suka kama wasu mutane suna ƙoƙarin canzawa shinkafar da aka bayar don talakawa, buhu zuwa na ’yan kasuwa, saboda a sayar a kasuwanni, a maimakon a raba wa jama’a kamar yadda gwamnati ta yi umarni ba. Wannan halayya ce ta sa jama’a da dama cire tsammanin ganin wani abu na alheri ya fito daga wajen ‘yan siyasa, wanda za a yi shi da zuciya ɗaya, kuma talaka ya shaida. An sha fito da tsare-tsare iri-iri don cigaban talakawa, amma a ƙarshe sai ya zama kamar an shuka dusa. Saboda yadda wasu ke babakere da almundahana akan abin, su yi wa kansu kasafi.

Mu kuma talakawa, mu ma da zarar mun samu dama an ɗora mu a kan wani sha’ani, sai ka ga mu ma tamu maitar ta fito fili. Har ma sai mu nemi zarta na ‘yan siyasar. Duk wanda aka ce ga wani kaso na jama’a a je a raba a ƙarƙashin ƙungiya ko wata al’umma a matakin unguwa, sai ka ga mutum ya karkatar da abin zuwa gidansa, sai wanda ya ga dama za a sam masa ɗan abin da bai taka kara ya karya ba. Shi ya sa malamai ke cewa, Allah yana ba mu shugabanni ne daidai da halayenmu, domin daga cikinmu ake zaɓo su. Don haka, babu wani abu da zai canza sai mun canza halayenmu da yadda muke mu’amala da juna. Ba daga yawan sharhi a kafafen watsa labarai ko zanga-zanga ba ne, matuƙar ba mu iya yaƙi da zuciyoyinmu ba to, talauci da yunwa ba za su rabu da mu ba.

Ga ita gwamnati kuma ta sassauta hanyoyin kasuwanci da tattalin arziki ta yadda talaka zai ji daɗi ya kuma shaida an samu canji, ba wai ta ɓullo da ayyukan da wasu ’yan tsiraru ne za su ci moriyarsa ba, kamar rabon kuɗi ko rabon abinci. Duniya ta wuce wannan tsarin, an daina raba wa mutane hatsi kamar kaji. Gara a sassauta farashi da wadata ƙasa da abinci, ta yadda zai iya saye cikin mutunci da rahusa, ba sai ya bi layi ko ya yi dambe a wajen rabon shinkafa ba.

Mun ji cewa, shugaban ƙasa ya bayar da umarnin a sayar da buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 50, a farashin Naira dubu 40, don sauƙaƙawa masu ƙaramin ƙarfi. Fatan mu shi ne wannan buri na Gwamnatin Tarayya ya cika har ta kai ga jama’a da dama sun iya mallakar abin da za su ci. Kuma kada ya zama wasu tsiraru kawai za a sayar wa, sauran kuma a sayar a kasuwar bayan fage ga ’yan kasuwa, yadda za su sa nasu farashin da suka ga dama. Domin kaɗan da aikin mayaudaran ‘yan Nijeriya, wajen cutar da ’yan uwansu, don cin moriyar kansu. 

Gwamnati ta yi ƙoƙari ta samar da wata hanya ta samar da tallafi ga kayan abinci, irin su hatsi da makamashi, da sauran muhimman abubuwan buƙatu na yau da gobe, don farashinsu na kasuwa ya sauka ƙasa sosai daga yadda yake a yanzu, domin talaka ya samu sauƙin rayuwa. Ta haka ne hankalin ‘yan Nijeriya zai kwanta, kuma zukatansu su yi sanyi daga tunzurin da suke yi a yanzu. Babu shakka na yaba da ƙoƙarin da Shugaban ƙasa Bola Tinubu yake yi na ganin ya daidaita al’amura, duk da ƙalubalen da shi ma yake fuskanta a gwamnatance, fiye da yadda ya zaci zai samu da hawansa mulki. In har za mu yi masa adalci mu yi wa kanmu, mun san cewa wannan matsala ba a lokacinsa aka fara ganinta ba, don haka kuma bai kamata a riƙa ɗora masa kowanne irin laifi ba. 

Buƙatar ‘yan ƙasa dai shi ne gwamnati ta ƙara jan ɗamara, ta canza matakan da take ɗauka, zuwa ga waɗanda za su kashe ƙishir ruwan talaka, ya samu abinci, ya iya zuwa aiki cikin sauƙi, ko ya fita kasuwancinsa cikin kwanciyar hankali, tattalin arziki ya riƙa juyawa yadda kowa zai amfana. Ba manyan ayyukan raya ƙasa ne damuwar talaka ba, cikinsa shi ne babbar damuwarsa. Kamar yadda marigayi Dr Adamu ɗanmaraya Jos yake cewa ciki jakar ɗan adam!

By ukarofi