‘Yan sanda sun musanta kashe masu zanga-zanga a Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta ce ba a samu asarar rayuka ba a jihar yayin zanga-zangar tsadar rayuwa wadda ta rikiɗe zuwa tarzoma a wasu jihohin ƙasar nan.

Kakakin rundunar ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

Kafin fitar da wannan sanarwa rahotanni daban daban sun bayyana cewar jami’an tsaro sun kashe masu zanga zanga biyu tare da jikkata wasu a ƙokarin jami’an tsaron na tarwatsa matasan da suka yi yunƙurin shiga gidan gwamnatin jihar.

Rundunar ta yi kira ga al’uma akan su yi watsi da jita jitar da ake yaɗawa cewa an harbi ma su zanga zanga a jihar.

Sanarwar da rundunar ta fitar ta kuma buƙaci al’uma akan su yi watsi da wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta inda aka nuna wani jami’in ɗan sanda na kwance a ƙasa ba rai, sakamakon harbin shi da abokin aikinsa ya yi a ƙokarin harbin masu zanga zanga a jihar.

“An ƙirƙiri bidiyon ne kuma ba a wurin aka ɗauke shi ba domin kuwa babu wani abu makamancin harbi a yayin gudanar da zanga-zangar.

“Maganar gaskiya ita ce jami’in tsaron da aka nuna a faifan bidiyon jami’in tsaron NSCDC ne da ya faɗo daga motar sintiri sakamakon hatsarin da motar ta yi a wurin zanga-zangar.

“Ba tare da ɓata lokaci ba aka garzaya da shi asibitin Koyarwa na gwamnatin Tarayya da ke Katsina, inda aka yi masa magani aka sallame shi,” in ji Sadiq-Aliyu.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su yi watsi da abin da ya bayyana a matsayin “labarin ƙanzon kurege”.

Daga ƙarshe ya buƙaci al’umar jihar akan su riƙa tantance bayanai ta sahihan kafafen yaɗa labarai na ‘yan sanda.

By ukarofi