Iyaye a Arewa ku ji tsoron Allah kan sauke haƙƙin yaranku

Assalamu alaikum, Manhaja. Barkan ku da aiki, muna muku fatan Allah ya ƙara muku ƙwazo, Ameen. Ina kuma muku addu’a Allah ya ƙara muku hikima da basirar aiki da kuma bunƙasa wannan jarida mai farin jini baki ɗaya.

A Arewa ne za ka samu gidan Almajirai da yara ba adadi, a Arewa ne za ka samu iyaye sun sake yaran su ana kwashewa ana sauya musu addini, a Arewa ne za ka samu gidan kangararru inda ake tara ɗaruruwan yara wai da sunan sun gagari iyayensu.

Kwanaki kaɗan da suka wuce wata baiwar Allah ta saka wani bidiyo a shafin sada zumunta na Tuwita, inda yara mata ƙanana waɗanda shekarunsu bai wuce 15 ba, suna neman a sanya musu alluran hana ɗaukar ciki.

A cikin bidiyon da aka tambaye su ko me za su yi da shi alhalin ba su da aure? sai suka ce talla ne aikin su.

Matuqar suka dawo gida ba tare da ciniki mai yawa ba, to koran su za a yi a gida.

Har yanzu jami’an tsaro ba su gama kwato yara da ’yan kudu (Ƙabilar Ibo) suka wawushe daga Arewa ba.

Waɗannan yara an ci zarafin da yawa daga cikin su kuma an keta musu haɗi. An tirsasa su bin addinin da ba su da alaƙa da shi.

Abin da zai ba ka mamaki shi ne, saboda tsabar rashin kula, iyayen waɗannan yara ba su nemi yaransu ba lokacin da suka ɓata.

Ba su haɗu suka sami gwamnati a kan cewa ana kwashe musu yara ba tare da sun san su waye ba.

Taimakon Allah ne kawai ya sa aka kama ɓarayin yaran. Idan da jami’an tsaronmu ba su kama su ba, to da shiru za ka ji.

Har ila yau, a Arewar mu ne aka bankaɗo gidajen kangararru. Irin waɗannan gidaje an yi su ne don karvar yara daga hannun iyaye da sunan sun kangare.

Jami’an tsaro sun gano cewa ana ketawa yara haɗi ta hanyar luwaɗi da su, hakazalika yaran na fama da cututtuka daban-daban.

Shin me ya sami iyaye ne a Arewa?

Ko iyaye sun manta cewa haihuwa kyauta ce daga Allah maɗaukakin sarki, wanda duk wanda aka ba shi to akwai haƙƙoƙi a kansa?

Ko iyaye sun manta cewa haƙƙin ciyar da yaransu, tarbiyyantar da su, tufatar da su, samar musu matsuguni da ba su ilimi duk ya rataya a wuyan su ne?

A kowani lokaci da iyaye suka yi wasa da haƙƙoƙin yaransu, to tamkar suna sake kuraye ne a cikin al’umma.

Waɗannan yara za su nemi su ci koda kuwa ta wani hanya ne. Za su nemi su sanya tufafi ko ta wani hanya, za su nemi su ji daɗin rayuwa ko ta wani hanya.

Yaron da ya rasa samun haƙƙoƙinsa a wurin iyayensa to ya samu matsala. Ba zai iya fahimtar daidai da kuma ba daidai ba. Tunaninsa ya samu tasgaro, cikin lokaci ƙarami zai iya zama bala’i a cikin al’umma.

Injiniya Mustapha Musa Muhammad. 08168716583.