Jama’a na kokawa da yawaitar tsibirin shara a birnin Kano

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Yanzu haka dai al’umma musamman a ƙwaryar Birnin Kano na kukawa da irin ɗimbin tarin shara da ta yi latutu a wurare daban-daban ba tare da ana kwashewa akan lokacin da ya kamata ba.

Tarin sharar dai ana iya ganinsu a gefen manyan hanyoyi da gefen kasuwanni da tsibi-tsibin tarin sharar a unguwanni da dama, duk kuwa da cewa akwai kamfanin shara da gwamnatin Kano ta yi yarjejeniya da shi ta miqa masa ragamar tsaftace Jihar Kano.

Mutane da dama da suka koka sun nuna cewa a halin yanzu da ake ciki ƙazanta ta yi yawa a Kano don ba za ka iya wata doguwar tafiya a ƙwaryar Birnin Kano ba ba tare da ka yi kiciɓis da tarin shara a kan titi ba.

Tarin sharar dai mafi yawa ake samunsa a wurare da dama da mutane ke yin hada-hada ko wucewa tana wari da hamami, wanda hakan ka iya zama barazana ga lafiyar al’umma musamman wajen yaɗa cuta.

Tun a baya ne dai Gwamnatin Kano ta bayyana yin yarjejeniya da wani kamfani da shi zai riƙa kwashewa da sarrafa shara a jihar har ma ta hannantawa kamfanin dukkan ma’aikatan kwashe shararta bayan rushe hukumar shara ta REMASAB da ta yi.

Sai dai tun ba a jima ba aka soma samun ƙorafe-ƙorafe daga ma’aikata sharan na rashin biyansu albashi da sauran matsaloli wanda yanzu har ta kai ga mutane na ganin gazawa sosai daga kamfanin wajen aikin kauda shara a Jihar Kano.

Mun yi ƙoƙarin tuntuvar kamfanin na kwashe shara a Kano, wato Cafegate don jin abubuwan da ke haifar da matsaloli da mutane ke kokawa akai na aikin ɗiban sharar amma har ya zuwa haɗa wannan rahoto jami’ar hulɗa da jama’a ta kamfanin ba ta ce komai ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *