Kwalejin Isa Mustapha Agwai ta Jihar Nasarawa ta rantsar da sabbin ɗalibanta

Daga JOHN D. WADA, a Lafiya

Sama da ɗalibai 700 ne suka ɗauki rantsuwar kasancewa ɗaliban Kwalejin Kimiya da Fasaha ta Isa Mustapha Agwai mallakar Gwamnatin Jihar Nasarawa dake birnin Lafiya, fadar jihar, wato wadda aka fi sani da Isa Mustapher Agwai Polytechnic a turance a lokacin wani babban bikin ɗaukar rantsuwar wanda aka gudanar a babban ɗakin taro na makarantar a ƙarshen makon da ya gabata. 

A jawabin shugabar makarantar, Dokta Justina Ajiode Kotso ta faro ne da taya sabbin ɗaliban murnar samun damar karatu a makarantar, inda ta ce an kafa makarantar ne da nufin samar da ingantaccen ilimin zamani da na addini don cigaban al’ummar jihar da qasa baki ɗaya, kuma a cewarta kawo yanzu kwalejin tana cimma burin sakamakon yaye ɗalibai dake bada gagarumin gudunmawa a fannin ilimi a jihar da ƙasa baki ɗaya. 

Ta bayyana cewa daga cikin kimanin ɗalibai 734 da suka samu gurbin karatu a kwalejin 400 za su yi karatun difiloma ne, yayin da 334 za su yi karatun babbar difiloma, inda ta buƙace su kada su yi wasa da wannan dama da suka samu. 

Ta kuma gargaɗi sabbin ɗaliban na zangon karatun shekarar 2021 da 2022 su tabbatar sun guje wa duk wata ɗabi’a da ka iya hana ruwa gudu a kwalejin kasancewar a cewarta kwalejin ba za ta ƙyale duk ɗalibi ko ɗaliba da aka kama da laifin ba. 

Dokta Justina Kotso ta kuma ja hankulan sabbin ɗaliban musamman dangane da shiga ƙungiyoyin asiri a ciki da wajen kwalejin inda ta shawarce su cewa maimakon haka su riqa kula da harkokin karatunsu a yayin zamansu a makarantar kaɗai. Su kuma guje wa sanya kayayyakin da zai zubar da mutuncinsu dama makarantar a idon duniya. 

Daga nan sai ta yi amfani da damar inda ta jinjina wa gwamnan jihar, Injiniya Abdullahi Sule dangane da tallafin da yake bai wa makarantar akai-akai da hakan ke haifar da ɗa mai ido a fannin ɗaukaka tare da inganta yanayin karatu a makarantar, inda ta buƙace shi ya cigaba da haka. 

Sauran abubuwa da aka gudanar a yayin taron ɗaukan rantsuwar sun haɗa da ɗaukar rantsuwar kasancewa ɗaliban kwalejin nagari da sabbin ɗaliban suka yi da sauransu.