Gwamnonin APC na zawarcin Wike

Daga BASHIR ISAH

Yayin da rikicin cikin gida na Jam’iyyar DP ke ƙara ƙamari, ita kuwa jam’iyya mai mulki, APC, na ƙoƙarin yin amfani da wannan dama wajen zawarcin Gwamnan Ribas, Nyesom Wike da sauransu.

An iya fahimtar hakan ne bayan da wata tawagar APC da ta ƙunshi gwamnonin APC da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar suka ziyarci Wike.

Gwamnan Legas, Sanwo-Olu da takwarorinsa na Ondo, Rotimi Akeredolu da Kayode Fayemi na Jihar Ekiti da sauransu, na daga cikin tawagar ta ziyarci Wike ɗin a Juma’ar da ta gabata.

Ana raɗe-raɗin cewar dalilin ziyarar shi ne, don zawarcin Wike da sauran ‘yan Jam’iyyar PDPn da ransu ya ɓaci game da harkokin jam’iyyar a kan su zo su haɗe da jam’iyya mai mulki a haɗa ƙarfi sannan a tunkari zaɓen 2023 tare.

Kafin wannan lokaci, rahotanni sun nuwa cewa, Tinubu da Wike sun gana a ƙasar Faransa bayan da Atiku Abubakar ya zama ɗan takarar Shugaban Ƙasa na PDP.

Kodayake dai, mai magana da yawun Tinubun, Tunde Rahman, ya fito ya ƙaryata hakan.

An ruwaito Wike ya ƙi sauraron wasu ‘yan aiken da Atiku ya tura masa kwanankin baya sa’ilin da ya kai ziyara ƙasar Turkiyya.