Hare-haren ta’addanci a kan ayarin motocin Buhari da na Kuje

A baya-bayan nan ne ’yan ta’adda suka kai hari a Cibiyar Gyaran Hali da ke Kuje, babban birnin tarayyar Abuja, inda suka kuvutar da fursunoni kusan 600, wanda 64 daga cikinsu ’yan ta’addar Boko Haram ne. Harin wanda ya ɗauki tsawon sa’o’i da dama ya yi sanadin mutuwar mutane biyar da suka haɗa da jami’an hukumar NSCDC waɗanda ba su ɗauke da makamai da kuma fursunoni huɗu. A yayin da suka isa wurin da yawa a kan babura, an ce ‘yan ta’addar sun yi amfani da bama-bamai wajen rusa katangar gidan yarin.

A cewar hukumomin wurin, jimillar fursunoni 879 ne suka tsere a lokacin wannan mummunan harin. An sake kama 443, fursunoni 551 a halin yanzu suna waje kuma 443 na tsare.

Jami’an gidan yarin ta Kuje sun kuma tabbatar da mutuwar fursunonin guda huɗu, yayin da wasu 16 suka samu raunuka daban-daban kuma suna jinya a wani asibiti da ba a bayyana ba a birnin. Bayan ya ziyarci wurin da aka kai harin, Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (mai ritaya) ya ce, game da maharan, “mai yiwuwa su ’yan Boko Haram ne saboda muna da adadi mai yawa na waɗanda ake zargi da Boko Haram a tsare, kuma a halin yanzu ba za mu iya gano ko ɗaya daga cikinsu ba. Ina tsammanin suna kusan 64 a gidan yarin kuma babu ɗayansu a yanzu. Dukkansu sun tsere.”

Harin wanda ake kyautata zaton ƙungiyar Boko Haram ce ta kai, ya faru ne a ranar da ’yan ta’addan suka kai hari kan ayarin tawagar jami’an tsaro da masu taimaka wa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari kan harkokin yaɗa labarai a hanyarsu ta zuwa Daura, mahaifar shugaban ƙasar gabanin bikin Sallah. An bayyana jikkata mutane biyu a harin. Rahotanni sun bayyana cewa, harin ya faru ne a kusa da Dutsinma a Katsina kuma ya nuna ’yan ta’addan da suke da ’yanci a yankin Arewa maso Yamma ba tare da mutunta wata hukuma ba, har ma da shugaban ƙasa.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Garba Shehu ya fitar, ya ce, “maharan sun buɗe wa ayarin motocin wuta ne daga inda suka yi musu kwanton ɓauna amma sojoji da ‘yan sanda da jami’an DSS da ke tare da ayarin sun daƙile. Wasu mutane biyu da ke cikin ayarin motocin na samun kulawa sakamakon ƙananan raunukan da suka samu. Duk sauran ma’aikata da ababan hawa sun isa Daura lafiya.”

Wannan harin ya nuna wata babbar alama na damuwa domin yana aikawa da mummunan saƙon cewa, wataƙila babu wanda ya isa ga ‘yan ta’adda kuma a gaskiya su ne ke da rinjaye a yaƙi da ta’addanci. Duk da cewa shugaban baya cikin ayarin hakan ba ya alamta komai. A kowane ma’auni, wannan babban rashin fahimta ne da gazawar aiki ba wai kawai ta hanyar tsaron shugaban ƙasa ba, har ma da manyan jami’an tsaro a ƙasar. Shin jami’an tsaro ba su san cewa a yanzu ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda sun fara kai farmaki a wannan yanki na jihar Katsina ba ne?

Harin da aka kai a gidan yari na Kuje wanda ya sa ɗaruruwan masu taurin kai da kuma ’yan ta’adda 64 suka tsere, abin takaici ne kamar harin da aka kai wa ayarin motocin shugaban ƙasa. Ya haifar da tambayoyi masu tarin yawa game da dalilin da ya sa ake ɗaure ‘yan ta’adda a Kuje, wani matsakaicin gidan yari maimakon a wani wurin da ya fi tsaro. Shin wannan al’ada ce ta hukumomin gidan yari kuma wane ne ya yanke shawarar yin hakan?

Akwai kuma rahotannin da ke cewa hukumar tsaron ƙasar ta yi gargaɗin kai hari a gidan yarin. Akwai buatar hukumar SSS ta yi ƙarin haske a lokacin da ta samu wannan bayanan, kuma ministan babban birnin tarayya ya sani da kuma lokacin da aka faɗa wa shugaban ƙasa.

Yanzu dai ba abin yarda ba ne ga masu riƙe da madafun iko su yi Allah wadai da waɗannan hare-haren ta’addanci. Suna buƙatar a yi musu hisabi. A ra’ayin wannan jarida, rashin tsaro da ake fama da shi a qasar nan ya yi ƙamari, domin babu wanda aka kama da laifin ta’asar taɓarɓarewar tsaro. Kuma wannan ya koma kan matakin da Shugaban ƙasa ya ɗauka na ƙin sauke manyan hafsoshinsa na farko daga muƙamansu duk da taɓarɓarewar tsaro a lokacin mulkinsu. Saƙon da shugaban ƙasa ya aikewa hafsoshinsa a wancan lokaci da kuma yanzu shi ne, duk yadda abubuwa su ka yi muni ba za a tuhume ku ba.

A matsayinsa na shugaban askarawan ƙasa, a ƙarshe shugaban ƙasa ne ke da alhakin rayuka da dukiyoyin kowane ɗan Nijeriya guda. Ya zama zavin shugaban ƙasa kada ya sake fasalin jami’an tsaro da ɓullo da aikin ’yan sandan jihohi inda gwamnonin za su iya ɗaukar wasu ayyuka. Muna da ra’ayin cewa babu wani saƙo mai ƙarfi da shugaban ƙasa zai iya aika wa hafsoshinsa da kuma shugabannin hukumomin tsaro cewa halin da ake ciki na rashin tsaro a ƙasar nan bai amince da shi ba, kamar ya sauke ɗaya ko biyu daga cikinsu daga muƙamansu.