JAMB ta soke jarrabawar tantance masu ‘Direct Entry’ ta 2024

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba da Sakandire ta JAMB ta soke jarrabawar tantance masu neman shiga jami’a kai tsaye ‘Direct Entry’ ta 2024.

Wata sanarwa da aka wallafa a shafinta na Ɗ ranar Litinin, ta ce za a yi la’akari da wasu dalilai na shigar da masu Direct Entry maimakon sai sun yi jarrabawa.

Hakan dai ya zo ne kamar yadda hukumar ta kuma ce an tsara dukkan matakai domin fara shigar da manyan makarantun ƙasar nan.

Har ila yau, ta ce za a gudanar da bugu na 2024 na taron manufofin shekara-shekara da aka daɗe ana jira a jiya Alhamis.

Ministan Ilimi Tahir Mamman ne zai jagoranci taron manufofin 2024, wanda aka shirya yi a ranar 18 ga watan Yuli a Abuja.

Taron manufofin zai ba da izinin fara shiga wannan shekara.

Sanarwar ta X ta ce, “Ayyukan na bana kuma za a bayar da lambar yabo ta ƙasa da ƙasa ta NATAP-M Awards, inda duk wanda ya yi nasara zai karɓi Naira miliyan 500, sauran waɗanda suka yi nasara za su raba Naira miliyan 250 gaba ɗaya.