Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Hon. Musa Ahmed Mohammed shine Akanta Janar na Gwamnatin Jihar Nasarawa kuma tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar ne har sau biyu, wato daga shekarar 2007 zuwa 2015 bayan ya yi murabus daga aiki a Birnin Tarayya Abuja kenan.
A tattaunawar nan ya bayyana wa Wakilin Blueprint Manhaja a Jihar Nasarawa, JOHN D. WADA, game da yadda kawo yanzu gwamnan jihar ta Nasarawa mai ci yanzu, Injiniya Abdullahi Sule, ya kawo horo da inganci da kuma tsari cikin jagorancin jihar da hakan ya aza jihar a matsayin ɗaya daga cikin jihohin ƙasar nan da ake samun yawan masu zuba jari daga waje a kullum da sauransu.
Ga yadda tattaunawar ta kasance. A sha karatu lafiya:
Yaya za ka kwatanta ƙoƙarin cimma nasarori da Gwamna Abdullahi Sule ke yi a jihar Nasarawa kawo yanzu?
A gaskiya ko makaho yasan cewa a yanzu nasarori da ake samu a jihar nan tamu ta Nasarawa ta wuce misali kuma abu ne da ya cancanci wasu jihohi su yi koyi da shi.
Idan ka kalli fannonin nasarorin da suka haɗa da na mutane da manyan ayyuka da gine-gine da asibitoti da sauransu za ka ga ba shakka Gwamna Sule yana ci gaba da cika alƙawura da ya yi wa al’ummar jihar nan baki ɗaya.
Misali a fannin gine-gine da sauransu babu wata ƙaramar hukuma a jihar nan a yanzu da za a ce ba a gina mata sabbin hanyoyi da makarantu ba ko yi musu kwaskwarima ba. Idan batun bunƙasar al’umma ne kuma da ci gaban matasa zan iya faɗa maka da babban murya cewa a cikin shekara guda kacal da na yi aiki a gwamnatinsa Gwamna Sule ya tallafa wa sama da matasa 7,000 a fannin ɗaukar aiki da sauransu. Misali a kwanan nan ya (gwamnan) amince a ɗauki sama da malaman makarantun sakandare mutum 4,000. Kafin wannan ma ya amince a kwashe sama da malaman 1,000 inda ya kuma amince a kwashe ma’aikatan gwamnati na wucin-gadi wato Sasual Staff kenan a Turance su zama ainihin ma’aikatan gwamnatin jihar nan gaba ɗayan su.
Haka kuma gwamnan ya sake amincewa a kwashe kimanin matasa 1,560 a fannin kiwon lafiya kuma idan ka yi jimilar waɗannan ma’aikata sabbi da aka ba su ayyukan za ka lura cewa a cikin shekara gudan nan gwamnatin nan ta kwashe sama da mutane 8,000 a aiki. Tabbas wannan shugabanci ne nagari shiyasa nace ya kamata wasu jihohi su yi koyi da gwamnanmu don ace gwamnati cikin shekara daya kacal ta iya yin haka banda wadanda tayi a shekarun baya kenan ai ta cancanci yabo. Saboda haka zan ce a shekara ɗaya na Gwamna Abdullahi Sule a mulkin jihar nan karo na biyu ya yi rawar gani sosai.
Ko za ka iya ambato ire-iren ayyukan ci gaba da gwamnan ya aiwatar kawo yanzu da ka tabbata ya inganta ci gaban tattalin arzikin jihar nan kawo yanzu?
Kamar yadda ka sani da farko babu wata gwamnati da za ta iya cimma nasarori ba tare da an samu zaman lafiya ba. Na farko kafin komai sai da gwamnan ya tabbatar ana samun kwanciyar hankali da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar nan baki ɗaya. Bayan ya cimma wannan nasara duk da ba a rasa wasu ƙalubalen tsaro a wasu lokuta don haka rayuwa ta gada. Amma a fili za a iya cewa Gwamna Sule ya yi iya ƙoƙarinsa ta fannin zaman lafiyar. Ka ga a cikin birnin Lafiya ɗin nan ba lungu da za ka bi ba za ka gwamnati tana gina sabon hanya ko gyara tsofoffi ba kuma babban aikin a yanzu shi ne kamar yadda ka sani na gina babban gada irin na zamani da ake kira fly-oɓer a turance wadda ba a ganin irin sa a duka arewacin ƙasar nan ta tsakiya baki daya. Saboda haka me za mu ce game da irin wannan mutumin kirki da Allah ya bamu a matsayin gwamnan jihar nan saida muce mun gode kuma da ma’aikata da al’ummar jihar nan baki daya a kullum sai daɗa yaba masa suke yi dangane da waɗannan ƙoƙarin.
A matsayinka na wanda ya kasance ɗan majalisar dokoki da kuma na zartaswa a yanzu ta yaya za ka kwatanta yanayin aiwatar da kasafin kuɗaɗen jihar nan da wasu hidimomin a gwamnatin Injiniya Sule kawo yanzu?
To, da farko akan iya gano hakan ne ta fannin kyakkyawar dangantaka dake tsakanin duka fannonin gwamnati da muke da su wato ɓangaren shari’a da na dokoki da kuma na zataswar. Idan ka lura a cikin waɗannan shekaru 5 da gwamna Sule ya yi ba a taɓa samun matsala dangane da gabatar da kasafin kuɗaɗen wa matsalisar dokokin jihar nan ba. ‘Yan majalisar ba su taɓa fito sun yi bayyanai cewa an wuce ƙa’ida a wajen kasafin kuɗaɗen ko wani abu makamancin haka ba, shi ya sa muke cewa Gwamna Sule a yanzu yana ma wuce samani a shugabancinsa wannan a taƙaice kenan.
Kwanakin baya lokacin da Jam’iyyar APC mai ci a ƙasa ta bai wa gwamna Sule wani aiki na musamman da ya shafi ƙasa baki ɗaya ya dawo da wasu kuɗaɗe da ya rage wa gwamnatin tarayya inda jam’iyyar ta yaba masa matuƙa. Me za ka ce game da hakan?
Shi ya sa nace da farko shi mutum ne dake da horo ta musamman da ya shafi kuɗi kuma uwa uba yana da tsoron Allah a zuciyarsa. Don ka ga a duka tattaunawarmu da shi za ka ji yana ce min Barade (sarauta na kenan) ka ga ba ina duba yau ne kaɗai ko duniyar nan ba don dukan mu za mu bai da hisabin abubuwa da muka yi a duniyar nan ranar gobe. Kuma kasan ba kowane gwamna ne zai riƙa gudanar da mulki cikin tsoron Allah irin nasa ba. Shi ya sa nake cewa wannan yabo da jam’iyyar APC ta ƙasa ta yi masa dangane da hakan bai bani mamaki ba don na riga nasan irin mutum da Allah ya yi shi wato mai riƙon amana da gaskiya ne.
To a fannin ilimi da kiwon lafiya fa me za ka ce a taƙaice gwamnan ya yi a fannonin?
Gwamnatinsa ta kwashe sama da ma’aikatan jinya sama da 1,506 kamar yadda na bayyana a baya ta Primary Healthcare Agency kenan a Turance. Ya kuma amince a kwashe sama da sabbi ma’aikata 300 a asibitin ƙwararru na Dalhatu Araf dake nan birnin Lafiya kaɗai. Wadannan ma’aikata ne da za su inganta harkokin kiwon lafiya a jihar nan baki ɗaya. Ya kuma samar da dinbin ma’aikata tareda magunguna da sauran kayayyakin asibitoti musamman irin na zamani a cibiya dake kula da harkokin duka asibitotin jihar nan wato Hospital Management Board kenan a turance dake nan birnin Lafiya da dai sauran su da dama da lokaci bazai bari in bayyana maka duka ba. A fannin ilimi kuma ka ga a yanzu gwamnatin sa tana cigaba da gina sabbin makarantu da gyare-gyaren wasu da dama ako ina a fadin jihar nan baki daya.
Batun kuɗaɗen fansho da gratuity wani fanni ne da yawancin gwamnonin ƙasar nan suke da matsala da su. Me gwamnatin Sule ke yi don samar wa ‘yan fanshon mafita a jihar nan?
To, ka ga bayan biyan ‘yan fanshon kuɗaɗensu akai-akai Gwamna Sule yana kuma tabbatar sun samu duka haƙƙoƙinsu kuma suna ci gaba da yi masa godiya a kullum. A wata ɗaya shige nan wato watan 6 gwamnan ya amince aka ware zuzuruntun kuɗi har sama da naira biliyan 1 don biyan su wasu basussukan su da gwamnatotin jihar nan da suka shude suka rike musu wato daga shekarar 2009 zuwa 2010 kenan. Kenan anan za ka yarda da ni cewa ba kawai ma’aikatan gwamnatinsa ne kaɗai ke cin moriyar gwamnatinsa ba har da su ‘yan fanshon da sauran al’umma baki ɗaya kuma na tabbata kwanan nan zai cigaba da sake musu kuɗaɗen don biya su duka sauran kuɗaɗensu.
A ƙarshe a matsayinka na wanda ke kula da fannin kuɗin gwamnatin jihar nan me za ka ce game da gine-ginen masana’antu da kamfanoni da gwamnan ke ci gaba da ginawa a sassan jihar nan a yanzu. Ko hakan yana shafar tattalin arzikin jiha?
Ka ga bayan ma’adanai da ake kwasa a jihar nan a kwanakin baya ma akwai wata masana’anta da shugaban ƙasa ya zo ya ƙaddamar. Kuma ribar da muke samu shine ba kawai ana kwasa ne ana tafiya da su ba kwanan nan zamu fara sarrafasu anan jiha da hakan zai sa za mu ma iya dogara da kanmu ba sai mun jira kasafin jihar nan daga gwamnatin tarayya ba. Abin da gwamna Sule ke yi wa al’ummarsa kenan a yanzu yana tabbatar ne tattalin arzikin jihar nan a duka fannonin rayuwa sun inganta