Argentina ta doke Kolombiya inda ta lashe gasar kofin Copa America karo na 16, sai dai wasan ya samu tsaiko bayan anjinkirta na tsawon mintuna 80 saboda hargitsi a wajen filin wasa na Hard Rock.
Lautaro Martinez ne ya samu nasarar zurawa Argentina ƙwallo ɗayan, da ta ba ta wannan nasarar a mintina na 112, mintina bakwai kafin bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Kyaftin Lionel Messi ya sha kuka lokacin da aka maye gurbinsa a mintina 66 da fafatawa, bayan raunin da ya samu a idon sawunsa.
Masu shirya gasar sun ce magoya bayan da ba su da tikitin sun yi ƙoƙarin shiga cikin filin, inda suka bar wasu magoya bayan su jira na sa’o’i a cikin zafin Miami don buɗe ƙofofin.
Magoya bayansa da jami’an ‘yan sanda da jami’an tsaro sun yi arangama tare da kama mutane da dama. Magoya baya da yawa sun buƙaci magani daga ma’aikatan jinya.
A kan haka aka ɗauki mintuna 25 ana hutun rabin lokaci, saboda wani shagali da shahararriyar mawaƙiyar nan ta Colombia Shakira ta yi a filin wasa, matakin da kocin Colombia Nestor Lorenzo ya soki lamirin tun da farko.
Messi bai taɓa lashe babbar gasar ƙasa da ƙasa ba har sai yana da shekaru 34, kuma yanzu ya lashe uku a cikin shekaru uku bayan gasar Copa America 2021 da kuma gasar kofin duniya ta 2022.
Da wannan nasarar Argentina ta lashe manyan kofuna huɗu cikin shekaru huɗu a tarihin ta, inda ta lashe kofin duniya a 2022, Kofin Kudancin Amirka a 2021 da 2024 sai kuma Finalisima a 2022.
Bayan kammala wasan, an zaɓi ɗan wasan gaban Columbia James Rodriguez a matsayin gwarzon ɗan wasan gasar, sai Emi Martinez a matsayin gwarzon mai tsaron raga, sai kuma Lautaro Martinez a matsayin ɗan wasan da yafi kowanne yawan zura ƙwallaye da guda shida.
Wasan ƙarshen nan, ya kasance na ƙarshe ga Angel Dimaria, inda ya tabbatar da ajiye takalminsa ga ƙasar Argentina, amma zai ci gaba da bugawa Benfica kakar 2024/2025.