Jarumar Kannywood, Aisha Tsamiya, za ta yi aure gobe

Daga BASHIR ISAH

Gobe idan Allah Ya kai mu ne za a daura auren jarumar Kannywood, Aisha Muhammad Ali wadda aka fi sani da Aisha Tsamiya.

Katin gayyatar da MANHAJA ta samu ya nuna za a ɗaura auren ne tsakanin Aisha da agonta Alh. Buba Abubakar.

Auren wanda za a ɗaura da misalin ƙarfe ɗaya na rana bayan an sauko daga Juma’a zai gudana ne a Masallacin Sheikh Zarban, Kwanar ‘Yan Wanki kusa da gidan Tanko Yakasai, ‘Yankaba, Kano.

Ana sa rai da fatan wannan aure ya zama silar ƙulla zumunta tsakanin iyalan gidan Alh. Muhammad Yaya da na gidan Mal. Muhammad Abdullahi (B. Gwarzo) waɗanda suka kasance iyayen ango da amarya.

Yayin da ya rage kwana guda da ɗaurin auren, masoyan jarumar na ci gaba da nuna farin cikinsu gami da taya ta murna dangane da batun auren.