Kadaɗe ya daɗe a taron PDP

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Ba wani baƙon labari ba ne kasancewar a makon jiya yadda sunan wani matashi, Muhammad Suleiman Kadaɗe, ya shiga kafafen yaɗa labarai, saboda yadda linzamin sunansa na addu’ar daɗewa ya bayyana da zaɓarsa a matsayin sabon shugaban matasan babbar jam’iyyar adawa ta PDP.

Tun kafin zaɓen na ga hotunan matashin mai shekaru 25 da manyan ‘yan jam’iyyar ciki kuwa har da wanda ya ma ta takarar shugaban ƙasa a 2019 wato Atiku Abubakar. Duk da dai taro ne na zaɓen shugabanni na ƙasa na PDP da ta mulki Nijeriya daga 1999-2015, amma maganar matashin nan ta karaɗe filin taron tamkar a na son nuna yanzu dandalin siyasa na matasa ne ko ya na son tafiya da matasan.

In na zauna tsam ina tunani sai na ga shin shugancin kujerar matasa ta kowace ƙungiya ya zama lalle sai an samu mai ƙarancin shekaru ne ko dai in an samu wanda zai kare muradun matasan ya wadatar? Koma dai me za a ce aƙalla an fi buƙatar a samu duka biyu ga sabuntar jini ga kuma nagarta. Ga matashi Muhammad Kadaɗe lokaci ne zai nuna ɗaya ɓangaren na sa, wato ya cika matsayin karancin shekaru saura na nagarta.

A tarihin PDP, Kadaɗe ya karya tarihin da Abdullahi Maibasira ya kafa a 2013 zamanin tsohon shugaba Jonathan inda ya zama shugaban matasa ya na mai shekaru 30. A wancan taron ne a dandalin ‘Eagle’ da ke Abuja a ka samu ficewar manyan ‘yan jam’iyyar karkashin jagorancin Atiku Abubakar.

Waɗanda su ka gwale taron a lokacin sun kai gwamnoni 7 kafin su ragu su koma 5 inda tsohon gwamnan Jigawa Sule Lamido da tsohon gwamnan Neja Babangida Aliyu su ka cigaba da zama a PDP har zuwa wannan lokaci da na ke rubutun nan. Haƙiƙa waccar ficewar gwamnoni da shigar su jam’iyyar APC ya ba ta tagomashi har ta lashe zave a 2015 ƙarƙashin shugaban ƙasa mai ci Muhammadu Buhari. Gaskiya wancan taro na 2013 ya bar baya da kura amma duk da haka bai kawar da tarihin Abdullahi Maibasira daga Neja ba wanda ya maye gurbin tsohon shugaban matasan jam’iyyar da ya kai shekaru 60 a duniya a lokacin.

Duk wata siyasar da za a yi za ka ji a na maganar mata da matasa waɗanda su ke zama kan gaba a rumfunan zaɓe wajen kada ƙuri’a ko ma kare ƙuri’ar. Manyan ‘yan boko da su ka san daɗin jikin su ba su faye fitowa zaɓe ba ko da zarar sun ga dugu-dugu waje na neman yamutsewa sai su garzaya tudun mun tsira su na buga waya su ji yadda ta kaya. Wannan fa ya sa a ke jan hankalin matasa da kaucewa yarda a yi amfani da su a matsayin ‘yan bangar siyasa don ƙarshe a kan kuɗin da ba su wuce na marar tuwo ba su je su hallaka wani talaka ɗan uwansu ƙi su kan su su rasa ran su a dawo a na cewa ina amfanin baɗi ba rai.

Duk lokacin da ka ga matasa sun hargitse a fagen siyasa za ka taras ‘ya’yan talakawa ne kuma wani mai hannu da shuni ko ɗan jari hujja su ke yi wa aiki. Yayin da ‘ya’yan ‘yan jari hujja ke manyan makarantun kuɗi a ciki da wajen qasa, nan kuma ‘ya’yan talakawa su na ta doke-doke don kare muradun waɗanda ba su damu da makomar rayuwar su ba. Don in sun haye kujera shikenan sai a gamu a akwatin talabijin wato mota ta tashi daga tasha ta bule mutane da hayaƙi.

Wani abun lura ma su waɗancan yara na ‘yan jarida hujja da ke karatu, su na kammalawa gida, mota da aiki na jiran su. Tun da haka ne ina amfanin biyewa waɗanda kan su kaɗai su ka sani sun maida matasa makamashin hura wuta in ta kama su arce tudun mun tsira su na annashuwa da junansu. Ba ma wata adawar gaskiya tsakanin ‘yan jari hujja a kowace jam’iyya su ke don a bayan fage su na hulɗa da juna kuma matan su na ziyartar juna su na ta dariya sun mayar da talakawa mahaukata.

Shin ba ku taɓa gani ba manyan masu adawa da juna a fagen kamfen amma sun haɗa ‘ya’yansu aure su na ta kyakyacewa da dariya!?. Darasi ya dace duk matasa su koya su zama masu hangen nesa da mutunta iyayen su da kakanni kazalika da nuna kishin ƙasa ba Naira ko ‘yan jari hujja ba.

Tsohon shugaban majalisar dattawan Nijeriya a Jamhuriya ta uku, Iyorchia Ayu ya lashe zaɓen shugabancin babbar jam’iyyar adawar Nijeriya ba tare da hamaiya ba. Ayu ya rasa rawanin sa na majalsar dattawa a lokacin bayan nuna mara baya ga Mashood Abiola wanda a ka soke zaɓensa a ranar 12 ga watan yuni na 1993.

Ayu ya zama shugaban ne bayan fito da shi a matsayin ɗan takara daga shiyyar Arewa ta tsakiya, inda jam’iyyar ta tura muƙamin shugabancin na ta.
“Ba mulkin gargajiya mu ke yi ba don haka ba naɗa ni a ka yi ba, tsaida ni takara a ka yi daga yankin Arewa, kuma ya zama wajibi a kaɗa ƙuri’a ta nuna amincewa da zaɓa ta,” inji Ayu a zantawa da gidan talabijin na ARISE ya yi da shi kafin aiyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Babban abun da ya ke bakunan manyan ‘yan PDP shi ne caccakar jam’iyyar APC mai mulki da alwashin dagewa don amshe madafun iko a babban zaɓen da ke tafe a 2023.

Ga abun da tsohon shugaban jam’iyyar Bello Halliru ke cewa, “shugabanni nagari za su jagoranci jam’iyyar don dawowa mulki da yardar Allah.”

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a 2019 Atiku Abubakar, da waɗanda su ka nemi tikitin irin su Sanata Rab’u Kwankwaso sun halarci taron.

‘Yan jam’iyyar na nuna tura shugancin Arewa ba zai dakatar ɗan yankin daga neman shugancin ƙasa ba. Aliyu Bello shi ne shugaban matasan jam’iyyar na Kaduna da ke da kwarin gwiwar duk mai son takara a inuwar jam’iyyar zai samu dama.

Tsohon shugaban jam’iyyar Uche Secondus wanda ya gaza samun nasara a kotu ta dakatar da babban taron ya yi wa jam’iyyar fatar alheri amma da ɗaura aniyar ɗaukaka ƙara kotun qoli don neman a dawo da shi mulki ya ƙarasa wa’adinsa zuwa watan disamba.

Yanzu kallo ya koma kan jam’iyyar APC mai mulki wacce nan gaba za ta yi irin wannan babban taro bayan gudanar da hakan a matakin ƙananan hukumomi da Jihohi. Haƙiƙa an samu cikas a wasu Jihohi kamar Kano da Bauchi inda a ka samu mutum biyu na aiyana kan su a matsayin shugabannin jam’iyyar.

Shugaban kwamitin riko na APC Mai Mala Buni ya kafa wani kwamitin sulhu ƙarƙashin tsohon gwamnan Nasarawa Sanata Abdullahi Adamu da zai yi ƙoƙarin ɗinke wannan ɓarakar.

Zaɓen 2023 sai wanda Allah ya ba wa aron rai kazalika madafun iko ma duk na hannun Allah mahaliccin sammai da ƙassai.