Kasafin 2023 ya samu tazgaro a Majalisar Dokoki

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

A ranar Alhamis, Majalisar Dokoki ta Nijeriya ta gaza amincewa da kasafin kuɗi na 2023, kamar yadda ta tsara tun asali, sakamakon yadda ta ce, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya miƙa mata kasafin cike da tazgaro.

A jawabinsa yayin zaman majalisar, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya ce, an tsara Majalisar Dattawan za ta amshi rahoton Kwamitin Majalisar Kan Ƙudirin Kasafin Kuɗi na 2023, amma hakan ya gagara.

A cewarsa, “sakamakon wasu manyan ƙalubale da ake fuskanta, ba mu iya karvar rahoton kasafin na 2023 ba, kuma ba komai ya janyo hakan ba illa yadda kasafin ya zo hannun majalisa cike da wasu matsaloli.”

Ya ƙara da cewa, a jiyan nan (Laraba) kuma sai katsam majalisar ta sake samun saƙon Shugaban Ƙasa na neman a amince masa da ƙwarya-ƙwaryar kasafin kuɗi na gyaran fuskar kasafin kuɗin zuwa naira Tiriliyan 23.7.

Daga dukkan alamu dai wannan uzuri ya jirkita batun amincewa da kasafin kuɗi na 2023 kafin shiga sabuwar shekara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *