Daga AMINA YUSUF ALI
Babbar Kotun Tarayyar mai zaman ta a Kano ta yi amanta ta lashe inda ta kore umarnin da ta bayar na hana Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ciyo bashin kuɗi Naira biliyan 10.
Ita dai wannan qara Yusuf Iyaka Rabi’u, Darakta Janar na haɗakar ƙungiyoyi masu zaman kansu shi ne ya shigar da ƙarar inda ya nemi kotu ta dakatar da Gwamna Ganduje daga ciyo wancan bashin wanda ya yi ikirarin zai ciyo shi ne don samar da kyamarar tsaro a jihar Kano.
Waɗanda aka yi qarar su sun haɗa da, Antoni Janar na jihar Kano, Kwamishinan kuɗin da kuma kakakin majalisar dokokin jihar Kano.
Sauran sun haɗa da, Bankin Access, Ma’aikatar kuɗi ta Tarayya, Ofishin kula da basussuka da sauransu.
Idan ba a manta ba, a baya kotun ta taɓa ba da umarnin dakatar da gwamnan daga yin rancen kuɗin da yake son ya yi don kafa na’urori da kyamarorin tsaro.
Sai dai kuma yanzu haka Alƙalin kotun, Mai Shari’a Abdullahi Liman ya soke wancan tsohon hukuncin da kotun ta yanke ranar 1 ga watan Yuli bayan buƙatar da Lauyan waɗanda ake ƙara, Muhammad Dahuru ya shigar ga kotun ranar 7 ga Yuli, 2022 yana neman kotun da ta janye wancan umarnin na dakatar da Gandujen daga amso rancen.
Kodayake, shi ma Lauyan masu ƙarar, Badamasi Suleiman, ya tura takardun ƙorafinsa har guda biyar inda yake sukan lamirin Lauyan waɗanda ake ƙara a kan buƙatarsu na neman kotun ta janye wancan dokar da ta hana Ganduje ciyo bashin Naira biliyan 10.
Masu ƙarar suna ƙalubalantar Gandujen kasancewar bashin da ya yi niyyar rantowa ya sava da dokar amso bashi ta shekarar 2003 a kundin tsarin mulkin ƙasar nan, da kuma dokokin jihar Kano na shekarar 1968, a cewar su.
Wannan ƙara dai ta biyo bayan da Majalisar dokokin Jihar Kano suka sahale wa Gwamna Ganduje damar ranto Naira biliyan 10 daga bankin Access.