Tattaunawa ta musamman da Sa’in Daular Usmaniyya

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

‘Na duƙe tsohon ciniki kuma duk wanda ya zo duniya kai ya tarar!’ Wannan ɗaya ne daga cikin kirarin da ake yi wa noma, wacce ke taka muhimmiyar rawa wajen samar da abinci, rage zaman kashe wando da ma uwa uba bunƙasa tattalin arzikin ƙasa. Sai dai kash, duk da muhimmanci da tasirin da noma ke da shi ga al’umma, rashin ba wa ɓangaren kulawar da ta dace, musamman ma a yankin Arewa dake filin noma, ya sanya qarancin ayukkan ya yawaita a tsakanin ‘yan Arewa, abinci haka, dama sauran ƙalubalen dake akwai. Wakilin Blueprint Manhaja a Sokoto Aminu Amanawa, ya samu damar zantawa da manomi, Basarake, kuma tsohon kwamishinan aikin gona na jihar Sokoto Alhaji Muhammad Jabbi Kilgori sa’in Kilgori, da ya yi bayani sosai kan inda gizo ke saƙar.

BLUEPRINT MANHAJA: Muna so ka gabatar da kanka
DAKTA KILGORI: Sunana Dakta Muhammad Jabbi Kilgori, Sa’in Daular Usmaniyya, Shugaban Ƙasar Kilgori.

Wannan lamarin na noma takamaimai menene shi?
To shi noma kamar yadda aka sani, sana’a ce wadda aka ƙirƙiro tun lokacin da, kuma sana’ar noma na ɗaya daga cikin sana’o’in da ɗan adam ya faro domin ya ci da kanshi ya kuma kula da hidimominsa da sauransu, ta hanyar yin shuka ta hanyar noma ta hanyar gyarawa ta da sauransu. To wannan abu ne da ya faro tun zamanin zamunna, al’ada ce ta ɗan adam kuma a duk ƙasashen duniya ko ina ana noma, kuma a nan wajenmu shi ne babban jari na al’umma nan, ƙasashen mu na Nijeriya musamman a Arewacin Nijeriya, noma shi ne babban jigon tafiyar da rayuwar al’ummarmu. Wannan noma yana ɗaya daga cikin waɗannan suka taka rawa wajen kai Nijeriya a inda take, ma’ana an yi amfani da noma ne wajen haƙo ma’adanin ƙasa da ake amfani da su a ƙasar nan, a Arewacin Nijeriya. Allah ya albarkace mu da  ƙasan noma amma abubuwan suna ci gaba da komawa baya,

Kamar me kuke ganin ya sa sa mutanen Arewa suke yi masa riƙon sakainar kashi a noman?
Gaskiya dama kamar yadda ka faɗa shi noma tun farkon wannan ƙasa ta mu Nijeriya shi ne babban jigon tattalin arziki, kuma shi ne ya bayar da gudummawa ƙwarai da gaske wajen inganta tattalin arzikin Nijeriya da kuma jin daɗinta. Shi kansa man fetur kafin a samo shi, mun dogara da auduga, mun dogara da fata da dai sauransu, duk abubuwan da zamanin turawa farkon gwamnatin siyasa lokacin su Amadu Bello to lokacin duka waɗannan abubuwan su ne babban ginshikin tattalin arzik’i da ingancin rayuwar jama’a.

To amma daga baya lokacin da aka yi amfani da su aka tono man fetur to sai abubuwa suka taɓarɓare suka fara ja da baya a harkar noma, domin lokacin ya zo sadda man fetur a jikin shi ya yi yawa ya wanzu, kuma ana samun kuɗi da sauƙi, iyakarka kawai ka je ka yi fadanci gidan wani, ko ka je ka amshi takarda wajen wasu ka sami kuɗi. Don haka, a maimakon ka je ka yi noma to ga hanyar da za ka yi noma za ka samu kuɗi ka sayi abinci da kuma abin tattalin arziƙin rayuwa a keyin noma da ake buƙata. To wannan ya sa gwamnatoci su kansu basu yi rawar gani ba wajen kulawa da tarbiyyar al’umma, don al’umma ba za su ga turbar abinda ba zai ɗore ba, abinda bai da inganci ba zai zamo a’ala ba ba ga rayuwarsu da na bayansu.

Don haka ga gwamnatoci aka yi sakaci a siyo abinci a ba wa mutane, kamata ya yi da wuri a ba su ƙarfin gwiwa, jarin nan a mai sai ga noma, a ƙara inganta noman nan a ƙara sarrafa kayayyakin nan a inganta su, kamar yadda wasu ƙasashen Duniya suke yi.  Mu ciyar da kanmu, kuma mu ciyar da ƙasashe domin a samu. To maimakon haka, sai muka ɗauki cewa tunda dai ga mu muna arzikin gwamnatoci sai suka saki hanya suka kama shigowa da abinci da kayayyaki na more rayuwar jama’a, wanda da can ana nomawa nan, ko ana sarrafa su nan ya zamana daga baya sayo su a ke yi.

Saboda anga cewa akwai arziki ya wanzu kuɗi sun samu, albashi kashi-kashi an yi ta ba da garavasa albashi da kuɗin abubuwa da dama da kwangiloli ga su nan suna ta tafiya da sauƙi a samu. Noma yana da wahala, dama ɗan adam haka yake, idan ya ga inda sauƙi yake, can yake tafiya, amma kuma kamata ya yi ya hau turbar da ke ɗorewa. Don hakan ga wannan shi ya kawo taɓarɓarewar aikin noma, saboda an saki hanya, gwamnatoci maimakon su ɗora mutane tarbiyyar da za su riƙe noma ya zama shi ne babban jigo kamar yadda yake tun farko, duk ƙasashen duniya haka suka yi, ko sun sami fetur sai su ajiye shi gefe guda sai su bunkasa aikin noma, su yi amfani da kuɗin nan na fetur su bunƙasa aikin noma, su zama suna samun kuɗin sarrafa abinci suna fitar da abincin nan wajen.

Kuɗin man fetur nan ana ci gaba da hidimar asibitoci da sauran ayyukka na rayuwa maimakon a ba wa mutane su yi ta bushasha har a fara shigowa da abinci. To wannan shi ne maƙasudin abinda ya faru ga tattalin arzik’in Nijeriya saboda mun saki hanya a dai-dai lokacin da muka samu fetur, mun dogara da fetur bayan muna dogara da kayan noma da noma da muke yi da kiwo. Sai muka dawo, dan hakan ga abubuwa suka taɓarɓare har muka kawo kanmu yanzu inda har sai mun shigo da kayan abinci kala-kala, sai mun shigo da nama! Sai mun shigo da kifi, sai mun shigo da kayayyaki da dama, alkama, shinkafa ga su nan dai duka daga waje. 

Maimakon da can muke nomawa mu sayar mu ba wa wasu ƙasashe, to wannan shi ne ya kawo da man fetur da irinsu manja da sauransu. Duk nan ake tahowa a saye a biya kuɗin shiga, amma daga baya sai abin ya taɓarɓare ya kawo mu har yanzu da ake nan ana ta ƙoƙari. Man fetur shi kanshi farashinsa yana tangal-tangal kuma ƙarancin abinci da tattalin arziƙi suna wanzuwa har gwamnatoci suka shiga wani hali kamar yadda ake ciki yanzu.

Idan an saki hanyar da za s riƙa tun farko, noma ya zamo shi ne babban jigo babban jari, wanda daga gare shi za a iya samun komai, sai dai a riƙa amfani da kuɗin man fetur a riqa tallafa wa gona. Maimakon a tallafa mai, sai aka rushe aikin aka bawa mutane daɗi suka sagarce.

A kwanan baya, kafofin yaɗa labarai sun ambato shugaban ƙungiyar manoma na ƙasa yana kokawa kan yadda gwamnatoci a dukkanin matakai suke mayar da su saniyar ware, sai kuma a ɗayan ɓangaren ake ganin duk shekara a kasafin kuɗi gwamnatocin nan na ware maƙudan kuɗi a cikin ɓangaren noma kaman abin ba ya isa ne ga manoman, ko kuma me yake faruwa tunda dai ka tava riƙon ma’aikatar gona a baya?
Wato kamar yadda ka sani, ƙasashen Duniya ko’ina noma shi ake ba muhammaci, sannan kuma dole a tausaya wa manoma a ba su abinda aka ce, mussaman don a saukar da farashin kayan noma, su kum in sun noma su sayar da kayan cikin sauƙi, to abubuwan da suke faruwa kenan. Farko dai mun saki hanya, na biyu kuma da aka zo yanzu ana ta kasafin kuɗi, maimakon a yi abubuwan da za su inganta aikin gona, sai a ba da abubuwa su shiga hannun manoma. Sau da yawa za a ba da kayan noma cikin sauƙi ko a ba da motar noma, ko a ba da taki ko a ba da wani magani, ko a ba da wasu aiki sai ka ga kayan aikin nan maimakon a hannunta su su zama sun zo ga manoma na gaskiya waɗanda da a gona ma su noma sai ka ga abubuwa nan sun zo sun shiga wata hanya wadda ba ta kawo inganci ga aikin noma ba. Don haka, ga waɗannan su ne abubuwan da suke faruwa har ake samun ƙorafe-ƙorafe saboda an riga an saba da rayuwa ta daɗi, Wanda yake maimakon a ba da muhimmanci ga noma, ba a bayar ba. Wasu ƙasashen Duniya, manoma su ke kafa gwamnati kuma suke rushe ta. Don abinci shi ne  jari. Da yawa ƙasashen duniya za ka ga manoma na da ƙungiya mai ƙarfi kamar wannan ƙungiyar.

A ce an ba noma muhimmanci da a ce noma na da kaso me yawa wajen tattalin arzikinmu da za ka ga cewa, tana da tasiri. Wasu ƙasashe za ka ga cewa a ko menene sai an tuntuɓi manoma, amma nan ma wani ba ya son a ce shi manomi ne.  Don ce masa bawauye za a yi. Amma wata ƙasa idan an ce masa ai wannan manomi ne, sai ka ga kowa ya tadda kai ya ce ai wannan muhimmin mutum ne. Amma nan ga yanzu idan ka ce manomi kake, gara a ce ma kansila da a ce ma manomi ko ba haka ba?

Don ka fi kadari cikin mutane maimakon ko manomin nan shi ke biyan kansila albashi, saboda sai ya noma an samu tattalin arziki, an samu jari sannan kuɗin da za a samu a biya albashin ma’aikata da sauran ayyukka. Don haka, ga mu muke da muhimmanci noma, muka da darajar inganta noma, kuma muna sakaci da muhimmanci noma da ba shi tasirin da ya kamata wajen tafiyar da tattalin arziki.

Kowacce gwamnati ta taho tana cewa za ta faɗaɗa zata  faɗaɗa aikin noma da bunƙasa aikin noma, amma dai sai a ga abin bai samu ba. An yi ta samun gwamnatoci suna yunƙurin mai yawa amma kuma abin sai ya zo bai yi wani tasiri ba, saboda da ma manoma da sauran al’ummar ƙasa sun ɗauki noma ba abinda yake da wani muhimmanci ba. Tun da har ana iya siyo abinci, na mutum to ina ruwansa da zuwa gona? maimakon a ce a’a, abincin nan fa da ƙasa.

Ba noma shi aka tsaya ka nomi wanda ka ce har ka yi rara ka bawa wasu suma su samu ko a sarrafa abin nan a juya shi ga wasu kayan da za mu iya sayarwa a ƙasashen waje mu samu kuɗin shigowa. To ka ga wannan ita ce tarbiyyar da muka rasa, shi ya sa har yanzu muke taƙainiya kowa na zargin wani. Gwamnati na zargin manoma, su kansu manoma ana zarginsu. Sau da yawa za a bawa manomi taki maimakon yasa a gona sai ya sayar. An baka taki cikin sauk’i amma sai ka je ka sayar.

To ka ga duk wannan ya danganci irin wannan matsalar tarbiyyar da muka gino shekara da shekaru na mutane su sami abinci ba sai sun je noma ba, sai dai kawai su je su yi lebaranci . Ƙila idan ka yi lebaranci ya fi zuwa ka je ka yi noma , da ka yi lebaranci, sai ka je ka sayi abincin da za ka noma ka huta, ba sai ka je ka wahalar da jikinka wurin wahalar noma da kiwo.

Na’am to ban sani ba a irin wannan yanayin duk da dai dukkannin ɓangarorin nan suna da laifi, da akwai mafita?
Eh to, mafita shi ne, mu koma can inda muka fito mu sake waiwaye baya mu gani shin ina muka saki hanya? Farko mu mai da wa noma muhimmancinsa wanda ya ke. Mu tabbata cewa an sa matakan bunƙasa aikin noma an ba da jari manoma su yi noma, an buɗa makarantun noma, an buɗa inda za a bawa manoma farashin kayan noma , sannan an buɗe massarafin inda za a dinga sarrafa kayan noma sannan an ba da tallafi ga aikin noma.

Duk ƙasashen Duniya da ka sani, duk wata ƙasa da ke son ta ci gaba, sai ta ba da tallafi ga ma’aikatan noma. Amurka   masu noma ko kashi goma basu kai ba, amma saboda ana ba da tallafi, ana ba da gudunmawar farashi kamin ka yi noma sai ka san nawa za ka siyar da buhun alkama, za a baka gona ace muna son ka noma buhu dubu, sai a baka gona a baka farashi, kana nomawa kana kai ga yawan da aka ce ka yi.

Kuma ka yi ka kai an baka farashi baka damu ba. Amma yanzu manoma cikin duhu suke aiki sai ga ka duk da kayan da za a baka gwamnati bata da hannu ta fitar da hannunta, wanda be kamata ba, sannan kuma an riga an an rage ƙarfin tallafin da ake bayarwa.

Yanzu ko menene manomi sai ya je ya siye shi kasuwa, musamman yanzu takin zamani, mai makon abinda ake sayarwa dubu biyar ₦5000 dubu shida ₦6000 sai ka ga taki kasuwa ya kai dubu ashirin har da ɗoriya in gantacce ne. To ka ga wannan abubuwan da waɗanda gwamnati ya kamata ta kula da su , suna dole a ba da tallafi ga aikin noma, dole a ƙarfafa, dole a ci gaba da bincike da wayar da kan mu manoma da shigowa da ingantattun hanyoyin noma da kuma ba da farashi mai armashi. Duk abinda ake son a noma yanzu kamar alkama ko masara ko shinkafa ko gero kamata ya yi akwai farashi a baka kwaliti a ce ka za, ga inda muke son ka noma ga shi ana saida maka idan ka noma buhu kaza, to farashinsa kowanne kaza. Don haka, kai za ka kwatanta gonarka, shin za ta noma buhu ɗari?
Idan ka noma buhu ɗari ka amshi iri ka amshi taki ka yi aikin noma riban nawa za ka samu. Idan ka ga ribar nan tana da tasiri da gudu za ka nomawa amma idan ka ga babu tasiri, kana zuwa ka yi? Don haka ga waɗannan abubuwa gwamnatoci ke tsara su, don idan gwamnati bata tsara su ba, ba wanda zai iya tsara su, saboda kowanensu in ka bar harkar noma ga y’an kasuwa ko waɗanda yake so yake yi. 

Don ga su nan da dama kana gani ko wajen sayar da kayan noma za ka ga ana ta almundahana ana ta abubuwa sai ka ga masu sai dai buhuhuwa an zo an samu buhu ruwan zafi an zo an zuba to duk wadannan abubuwa bai kamata ba, kamata ya yi kilo a auna nauyin tsaba ka biya gwamnati. Ya kamata ta fitar da ma’auni ta fitar da farashi don za ta iya biya a samo gota ga kamfanoni sarrafa kayan gona na k’asashen waje waɗanda ka buƙatar kayan nan a zo a tsara yadda za a yi.

Don haka, ga wannan babban aiki ne dole sai gwamnati ta sake komawa mun koma shekara arba’in ko hamsin da sunka wuce mun duba shin menene muka yi lokacin nan?

Da abubuwa suka noma shi ne ginshiqin tattalin arziki, ko yanzu suna da tasiri waɗannan matakan don babu abinda yake a wannan lokacin sai bawa manoma tallafin kayan gona da basu ingantattun kayan noma basu jari ba su farashi sannan da kulawa da sha’anin da ya shafi zirga-zirga a bud’a hanyoyin ciniki a buɗa hanyoyin sufuri a buɗa hanyoyin da za su sa a samu bayanai da sauransu ta rediyo da talabijin da sauransu, to ka ga waɗannan abubuwa su ne suke sa aikin noma ya ci gaba. Don haka, idan mun yi su in sha Allahu za mu  cimma gaci.

To mu na godiya.
Ni ma nagode.