Kotu ta bai wa DSS damar ci gaba da tsare Mamu har tsawon kwanaki 60

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Talata ta bai wa Hukumar ‘Yan Sandan Farin Kaya, DSS damar su cigaba da riae Tukur Mamu, mai sasanta wa tsakanin ‘yan ta’adda da iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna, har tsawon kwanaki 60.

Mai Shari’a Nkeonye Maha ya bada umarnin ne biyo bayan lauyan hukumar tsaro ta farin kaya ya nemi da a ƙara musu lokaci don cigaba da binkice akan Tukur.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa NAN ya ruwaito cewa ‘yan sandan Masar sun kama Tukur Mamu tare da iyalansa a ranar 6 ga watan Satumba, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Saudiyya domin yin Umara, daga ƙarshe suka dawo da su gida Nijeriya.

A ranar Lahadin ta gaba ta jami’an na hukumar ta DSS suka jawa ‘yan Nijeiya kunne kan tufar albarkacin bakin su akan kama Tukur Mamu.