Kotu ta raba auren shekara ɗaya saboda rashin soyayya

Kotu

Wata Kotun Shari’ar Musulinci da ke Ilorin, Jihar Kwara ta raba wasu ma’aurata da aka ɗaura aurensu watanni 12 da suka gabata.

Alƙalin kotun, Abdulƙadir Umar, ya ce, matar mai suna Roimat Qodir ta roƙi kotun ta kashe aurenta da mijinta Abdulƙadir AbdulRazak, saboda ba ta sonsa.

Bayan alaalin ya tambaye ta ko tana da juna biyu, ta musanta hakan.

Shi ma dai mijin ya bayyana wa alƙalin cewa ya amince da buƙatar matar, kuma ko a lokacin ta so za ta iya tafiya.

A ƙarshe dai kotun ta raba auren, tare da bai wa matar umarnin yin iddar watanni uku kamar yadda addinin Musulinci ya tanada.