Kotu ta raba Dogara da Majalisar Wakilai saboda sauya sheƙa

Daga BASHIR ISAH

A ranaar Juma’a Babbar Kotun Abuja ta tsige Honarabul Yakubu Dogara daga matsayinsa na ɗan Majalisar Wakilai tare da bayyana kujerar tasa babu kowa a kai.

Alƙalin kotun, D.U. Okorowo, ya yanke hukuncin cewa sauya sheƙa da Dogara ya yi daga PDP zuwa APC hakan ba daidai ba ne, don haka ya ce wajibi ne ya sauka daga kujerarsa.

Dogara ya koma APC ne bayan samun nasarar sake lashe zaɓe ƙarƙashin jam’iyyar PDP a 2019.

Ana kyautata zaton ‘yar tsamar da ke tsakaninsa da Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, na ɗaya daga cikin dalilin da suka sanya shi ficewa daga PDP, jam’iyyar da ya shige ta ƙasa da shekaru biyar da suka gabata.

Dogara na wakiltar mazaɓar Bogoro/Dass daga Jihar Bauchi ne inda aka zaɓe shi a matsayin Kakakin Majalisar Wakilai tsakanin 2015 da 2019.

A ranar 24 ga Yulin 2020 Dogara ya bar PDP ya sauya sheƙarsa zuwa tsohuwar jam’iyyarsa ta APC.

Idan dai za a iya tunawa, a 2018 ne Dogara ya fice daga APC zuwa babbar jam’iyyar hamayya ta PDP bayan da ruwa ya yi tsami tsakaninsa da gwmanan Bauchi na wancan lokaci, Mohammed Abubakar.

Cikin wasiƙar murabus da ya aika wa shugaban PDP na gundumar Bogoro ‘C’ mai ɗauke da kwanan wata 24 ga Yuli, 2020, Dogara ya nuna yadda ya ce ya taimaka wa Gwamna Bala Mohammed wajen samun nasara a 2019.