Ku gaggauta kuɓutar da duka waɗanda ke hannun ‘yan ta’adda, umarnin Buhari ga jami’an tsaro

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bai wa shugabanni da hukumomin tsaron Nijeriya umarni a kan su gaggauta kuɓutar da duka mutanen da aka yi garkuwa da su.

Umarnin Buharin ya taso ne sakamakon ƙaruwar harkokin ‘yan ta’adda da barayin daji a sassan ƙasa.

Mai Bai wa Buhari Shawara Kan Harkokin Tsaro, Major-General Babagana Monguno (mai murabus) ne ya bayyana haka a ranar Alhamis yayin da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Tsaro tare da Shugaba Buhari a Fadar Shugaban Ƙasa.

A cewar Monguno, “Buhari ya nuna rashin jin daɗinsa kan matsalolin tsaron da muka samu baya-bayan nan a ƙasa, musamman waɗanda aka rasa rayuka da dama da kuma yin garkuwa da gomman mutane.

“Ba wai iya waɗanda aka sace a harin jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja ba, har da ma waɗanda aka yi garkuwa da su a wasu sassan ƙasa.”

Ya ƙara da cewa, Shugaba Buhari ya ba da umarnin gaggawa kan jami’an tsaro su hanzarta ceto waɗanda ɓarayin dajin ke tsare da su ba tare da sun ji ko ƙwarzane ba.

Daga nan ya ce, ya miƙa wasu shawarwari ga Shugaban Ƙasa waɗanda za su taimaka wajen yaƙi da matsalolin tsaron, kuma Buhari ya karɓa yana nazarinsu.