2023: Ba yanzu zan fito takara ba, inji Jonathan

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya shaida wa masu neman ya fito takarar shugaban ƙasa a 2023 cewa, ba yanzu zai fito ba.

Ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke karɓar baƙuncin ɗimbin magoya bayansa, waɗanda galibinsu matasa da mata ne da suka kai ziyara ofishinsa da ke Abuja domin gudanar da tattakin haɗin gwiwa.

Sun lallashe shi ya ayyana takarar shugaban ƙasa a 2023, yayin da shugabannin magoya bayan da ke ɗauke da alluna suka yi ta neman tsohon shugaban ya dawo kan karagar mulki a 2023. Sun yi alƙawarin za su yi aiki domin ganin ya samu nasara a zaɓe.

Wasu daga cikin fastocin da ke ɗauke da hotunan Jonathan sun rubuta ‘GoodLuck Jonathan, dole ne ka tsaya takara, muna buƙatar ka dawo da Nijeriya yadda ta ke.’

Suna jayayya cewa tsohon shugaban ƙasar yana da tsarin da zai dawo da martabar Nijeriya tare da bai wa dukkan ‘yan Nijeriya jin daɗin zama.

Da ya ke mayar da martani, Jonathan ya yaba wa ɗimbin jama’ar da suka bada goyon baya da ziyarar da suka kai.

Ya ce, “Eh, kuna kirana ne in zo in bayyana. Ba zan iya gaya muku ina eh ko a’a ba a yanzu ba amma har yanzu ana cigaba da gudanar da harkokin siyasa.”

Wasu ƙungiyoyi ma sun yi kira ga Jonathan ya tsaya takara. A jiya ne ƙungiyar matasan Nijeriya masu sana’a a ƙasashen waje, NYPD, ta baiwa Jonathan wa’adin mako guda ya bayyana a takarar shugaban ƙasa a 2023 ko kuma a kai shi gaban kotu.

Ƙungiyar wacce ta ƙunshi matasa ƙwararru a lasashen waje ta ƙunshi ’yan Nijeriya daga ko ina a cikin lasar waɗanda ke ƙasashe daban-daban.