Kotu ta tisa keyar shugaban EFCC, Bawa zuwa kurkuku saboda rashin ɗa’a

Daga BASHIR ISAH

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta ba da umarnin tisa ƙeyar Shugaban Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC), Abdulrasheed Bawa, zuwa kurkuku bisa laifin raina umarnin kotu dangane da gazawar hukumarsa wajen cika umarnin kotu

Alkalin kotun, Mai Shari’a Chizoba Oji ne ya yanke hukuncin tura Bawa gidan kaso a ranar Talata.

Alƙalin ya ce shugaban EFCC ya ƙi martaba umarnin da kotun ta bai wa hukumarsa ranar 21 ga Nuwamban 2018, inda kotun ta umarci hukumar da ta maida wa wani da ya shigar da kara a kanta motarsa ƙirar Range Rover (Supercharge) da kuɗi miliyan N40,000,000.00.

Bisa wannan dalili ne Alƙalin ya ba da umarnin a kai Bawa gidan yarin Kuje saboda rashin ɗa’a ga kotu har sai ya cika umarnin.

A cewar Oji, “Sufeta-Janar na ‘Yan Sanda zai tabbatar da an bi wannan umarni na kotu.”

Yayin shari’ar, Alƙalin ya yi watsi da bayanin lauyan EFCC, Francis Jirbo, da ya gabatar wa kotun don kare halin rashin ɗa’ar da Bawa ya nuna wa kotu.