Ku daina kiran mu da sunayen ƙasƙanci – Shugaban Gidauniyar Zabaya

Daga AMINU AMANAWA a Abuja.

Shugaban Gidauniyar Zabaya ta Ƙasa, Jake Epelle, ya nuna damuwarsa kan yadda al’umma ke kiran mutanen da ke da lalura ta musamman da sunaye marasa daɗi da kuma nuna cin zarafi ƙarara.

Jake na bayyana hakan ne a Abuja yayin wani taron horar da menama labarai 20 da ƙungiyar fito da dabarun samar da cigaba a aikin jarida ta CJID ta shirya kana ya gudana a Novare Mall da ke Abuja.

Jake ya bayyana cewa abin takaici ne matuƙa maimakon a tausaya masu sai a buge da kiransu da sunaye daban-daban a harsuna daban-daban.

“Kafofin yaɗa labarai da ’yan jaridu sune sahun farko da ke kiran mu da wasu sunaye marasa daɗi, misali sai kaji an kiramu da ‘Nakasassu’ ko mutane masu buƙata ta musamman wanda sam bai dace ba”.

“Ko kuma ace mana zabaya! sam bai dace ba a kawai a kiramu da mutane masu da lalurar zabayanci.

A cewarsa, ba wata nakasa da suke da domin suna da lafiyar aiwatar da komai tamkar masu lafiya, wasu lokuta ma har kwazon nasu ya haura na masu lafiya.

Da ya ke magantawa tunda farko shugaban cibiyar Tobi Oluwontola ya bayyana cewa sun shirya taron ne domin ilmantar da ’yan jarida hanyoyin da za su riƙa rahotannin da za su sanya a riƙa damawa da su a lamurran yau da kullum tamkar sauran al’umma.

Ita ma dai da ta ke gabatar da maƙala mai taken “Fahimtar mutane masu fama da lalura ta musamman” shugabar ƙungiyar da ke fafutuka kan mutane masu fama da lalura ta musamman na ƙasa Grace Jerry ta bayyana cewa akwai buƙatar al’umma su fahimci hanyoyin da za su riƙa mu’amalantar su, kuma ce masu da ake masu buƙata ta musamman sam bai dace ba domin ko masu lafiya ai naɗa tasu irin buƙatar.

“Misali kuɗi kowa na buƙatarsa kenan masu lafiya da ke bulatar kuɗinsu ba masu buƙata ta musamman don bane kan kuɗin?”.

Don haka a cewar ta manema labarai ya kamata su kasance sahun gaba wajen canja tunanin al’umma kan wannan halayyar.