Ku yi amfani da damar da arewa-maso-yamma ta samu na ƙarfafa nasarar ci gaba- Fall

Yayin da Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma da Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya ke yunkurin tabbatar da dorewar zaman lafiya a yankin, babban jami’in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya, Mohamed Malick Fall, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su yi amfani da damar da yankin Arewa-maso-Yamma ya samu masu yawa ta hanyar karfafa nasarar cimma muradun ci gaba mai dorewa (SDGs) da kuma kafa hanyar samar da ci gaba na dogon lokaci da magance matsalolin al’ummar yankin.

“Bari mu kuma shiga cikin babbar damar da yankin ke da ita don karfafa nasarorin da aka samu na SDGs da kuma kafa hanyar samar da ci gaba mai dorewa a yankin. Mu zabi ba da fifiko wajen daidaita rarrabuwar kawuna da haduwar juna don bunkasa dabi’un hakuri da mutunta juna da sulhu da mutuncin dan Adam.”

Ya bayyana hakan ne a taron farko na zaman lafiya da tsaro na yankin Arewa maso Yamma da ke gudana a ranakun 24 zuwa 25 ga watan Yunin 2024, a Katsina.

Fall ya lura cewa, don magance kalubalen da ake fuskanta a yankin Arewa maso Yamma yadda ya kamata, zai bukaci hanyoyin da za a bi a fannoni daban-daban a fannin ayyukan jin kai, ci gaba da gina zaman lafiya, wannan, a cewarsa, “Zai ba mu damar karfafa matakan tsaro ta yadda za a magance matsalolin da suka addabe su kamar karancin albarkatun kasa, magance zurfafa rashin daidaiton tattalin arziki, da magance rarrabuwar kabilanci da addini wadanda dukkansu ke da tushe.”

Ko’odinetan ya jaddada cewa, ya kamata mu mai da hankali wajen inganta harkokin gudanar da mulki tare da tabbatar da adalci, ilimi, samar da walwala, inda ya ce ta hanyar inganta huldar da ke tsakanin gwamnati da ’yan ƙasa, ita ce babbar yarjejeniya ta zamantakewa. Za mu iya ganin waɗannan tsare-tsaren suna canzawa ta hanya mai dorewa don ciyar da ajandar zaman lafiya a Nijeriya.

“A yau mun kuduri aniyar daukar matakan samar da zaman lafiya wanda zai ciyar da ajandar SDG gaba, da kuma gina Nijeriya wanda hakan zai bai wa kowa damar gudanar da ‘yancinsa da cikakken iko.

Majalisar Dinkin Duniya tana goyon bayan Nijeriya a kokarinmu na hadin gwiwa don tallafa wa daidaito, ‘yancin dan adam da wadata ga kowa da kowa,” a cewar Fall.

Taron mai taken “Haɗin Kai Tsakanin Yankuna Don Tabbatar Da Rayuwa Da Walwala A Yankin Arewa Maso Yammacin Nijeriya,” ya samu halartar Mataimakin Shugaban Kasar Tarayyar Nijeriya Sanata Kashim Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A jawabinsa na musamman, Shettima ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin sake mayar da jama’ar Pulaku muhallinsu a matsayin wani shiri na kishin kasa domin magance wasu matsalolin da ke haifar da rigingimu da rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma.

“Za a fara aikin gwajin ne a Jihohin Sokoto, Kebbi, Benue, Katsina, Zamfara, Neja da Kaduna”. Shettima ya jaddada cewa, “Sakamakon shirin ya hada da gina gidaje, tituna, makarantu da muhimman ababen more rayuwa, wanda ke nuni da kudurin gwamnati na samar da ci gaba mai dorewa da kuma dunkulewar kasa, lumana da wadata Nijeriya.”

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa Maso Yamma kuma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya jaddada muhimmancin hadin kan yankin wajen magance matsalar rashin tsaro. Ya kuma bayyana kokarin kungiyar gwamnonin Arewa maso Yamma wajen magance matsalolin da suka hada da tsaro, noma, da samar da wutar lantarki.

Gwamna Radda ya bayyana cewa, “Gwamnonin sun kaddamar da wasu tsare-tsare na tsaro a jihohinsu, kamar kungiyar Community Watch Corps da ke Katsina, domin yin aiki tare da jami’an tsaro.

Leave a Reply