Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Kwamitin daidaita iyakokin masarautun hakimai a jihar Katsina ƙarƙashin mai ba gwamna shawara kan ayyukan ƙananan hukumomi Alhaji Ahmed Rufa’i Safana.
Alhaji Umar Faruk Umar ya bayyana wa ‘yan kwamitin cewa, masarautar Daura na matuƙar yabawa da ƙoƙarin Gwamna Raɗɗa wajen warware dukkan wasu matsalolin al’umma da kan taso inda ya jaddada cewa masarautar Daura a shirye take ta aiwatar da dukkan shirye-shiryen gwamnatin jihar katsina na raya ƙasa.
Sarkin ya bayyana cewa masarautar Daura tsaye take wajen tabbatar da haɗin kai da gudanar da harkokin sarauta cikin tsari, ladabi da biyayya.
Alhaji Umar Faruq ya kuma yaba da kafa wannan kwamiti na daidaita iyakokin hakimai na jihar Katsina, ya ƙara da cewa, kafa kwamitin ya zama wajibi saboda ƙaruwar yawan al’umma da aka samu. Ya kuma shawarci ‘yan kwamitin da su tabbatar da adalci da riƙon amanar wajen sauke nauyin da gwamnati ta ɗora masu.
Tun farko, shugaban kwamitin, mai baiwa gwamna shawara a kan ayyukan ƙananan hukumomi, Alhaji Lawal Rufa’i, ya bayyana wa Sarkin cewa, kwamitin ya yanke shawarar kawo ziyar ban girma gare shi ne domin neman tubaraki da shawarwari don samun sauƙin sauke nauyin da gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa ya ɗora wa kwamitin.
Alhaji Lawal Rufa’i ya shaida wa Sarki cewa, kwamitin zai gudanar da aikinsa cikin gaskiya da riƙon amana, domin ta hakan ne duk wani tsari da za a fito da shi zai zamo mai amfani ga al’umma.
Alhaji Lawal Rufa’i ya ƙara da cewa, sakamakon aikin kwamitin zai taimaka wa gwamnatin jihar Katsina ta magance dukkan matsalolin iyakokin masarautun hakimai a jihar Katsina.
Mambobin Kwamitin sun haɗa da shugaban ƙaramar hukumar Mani Dr Yunusa Mohammed Bagiwa, da Danwairen Katsina, Dr. Sada Salisu Rumah, da Galadiman Daura, Alhaji Ahmadu Ahmadu Diddiri da wakilcin ma’aikatar shari’a da ƙasa da safiyo da kuma ta yaɗa labaru. Sai kuma ofishin sakataren kwamitin, Alh Abdulmumin Maidabino .
