Kwamitin karɓar tallafin Abba Gida-gida a kano ya tara sama da miliyan N500

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar NNPP reshen Jihar Kano ya sami jimillar kuɗi Naira miliyan dari biyar da goma sha daya da naira dubu dari biyu da hamsin da bakwai domin gudanar da yakin neman zaɓe da sauran harkokin zabe da za a gudanar a ranakun 25 ga watan Fabrairu da 11 ga watan Maris 2023.

Wannan na cikin wata sanarwa da babban mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen NNPP a Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana wa manema labarai ta ce, bayan taron liyafar cin abinci da jam’iyyar ta gudanar a daren Lahadi a Afficent Event Centre da ke Kano.

A cewar sanarwar, shugaban kwamitin tara kuɗaɗen na NNPP a Kano Hon. Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila, wanda ya lissafo waɗanda suka bayar da tallafin, ya bayyana jin daɗinsa kan tallafin da aka samu, inda ya jaddada cewa, hakan wata shaida ce da ke nuna cewa mutanen Kano suna buƙatar canji,

Hon. Kawu Sumaila ya kara da cewa za a yi amfani da tallafin ne wajen tallafa wa yaƙin neman zaɓe da kuma harkokin zaɓe.

Sanarwar ta ruwaito ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP, Engr. Abba K. Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-gida ya bayyana cewa irin goyon bayan da yake samu shaida ce mai nuni da mutanen Kano masu kishi na buƙatar sabon salon shugabanci a jiha da ƙasa baki ɗaya.

Abba Gida-Gida ya jaddada ƙudirinsa na ganin an samar da shugabanci nagari wanda kowane ɗan ƙasa kuma mazaunin jihar Kano zai ci gajiyar tsarin shugabanci nagari.

Sanarwar ta kuma bayyana kalaman ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda a jawabinsa na musamman ya ce ‘yan Nijeriya su na da zaɓi kan wanda za su zaɓa ko nagari ko akasin hakan.

Inda ya ce masu kaɗa ƙuri’a suna ƙara wayewa a kowace rana, kuma shawarar da suka yi na zaɓen NNPP ita ce kaɗai mafita gare su saboda halin da ƙasar ke ciki.

Haka kuma, Babban Mai ƙaddamarwa Hon. Tijjani Abdulkadir Jobe wanda kuma ɗan majalisar wakilai ne mai wakiltar mazaɓar Dawakin Tofa da Rimingado da Tofa a majalisar wakilai ta tarayya ya bayar da gudunmawar kuɗi naira miliyan hamsin. Hon. Jobe wanda ya fito daga mazaɓar Gwamna Ganduje kuma a halin yanzu yana takara da ɗan gwamnan, ya bayyana salon siyasar Sanata Kwankwaso a matsayin na biyu a cikin manyan ‘yan siyasar Najeriya.

Sanarwar ta bayyana wasu daga cikin waɗanda suka bada tallafin da suka haɗa da Dr. Abdulmumin Jibrin Kofa wanda ya bada gudunmawar Naira miliyan 25, Alh. Sani Muhammad Hotoro, Naira miliyan 20, Alh. Nasiru Muhammad Danfaranshi, Naira miliyan 20, Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum, Naira miliyan 10, Hon. Badamasi Ayuba, Naira miliyan 10 da dai sauransu.