Dalilin IPMNAN kan dakatar da sayar da fetur a gidajen mai

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Dillalan Fetur ta Nijeriya (IPMAN) ta dakatar da sayar da fetur a gidajen mai a faɗin ƙasa.

Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin wasiƙar da ƙungiyar ta aike wa mambobinta mai ɗauke da sa hannun shugabanta, Mohammed Kuluwu da kuma kwanan wata 6 ga Fabrairun 2023.

A cewar ƙungiyar, in ban da asara babu abin da manmobinta za su samu muddin suka ci gaba da sayar da fetur a cikin wannan yanayi.

Wasiƙar ta ce, “Biyo bayan halin matsin da ake fuskanta wanda ya shafi hada-hadarmu da janyo mana asara, ana umartanku da ku dakatar da sayar da mai a gidajen mai baki ɗaya da ɗauko dabon kaya har sai baba ta gani.”

Majiyarmu ta ce IPMAN ta gana da wasu masu ruwa da tsaki a ranar Talata don tattauna yadda za a samu mafita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *