2023: Maidoya ya gana da shugabannin NNPP na ƙananan hukumomi a Nasarawa

*Ya buƙace su su riƙe amana

Daga JOHN D. WADA, a LAFIYA

Don tabbatar da nasarar jam’iyyar NNPP a duka matakai a jihar Nasarawa da ƙasa baki ɗaya, ɗan takarar kujerar gwamnan jihar Nasarawa a inuwar jam’iyyar NNPP, Abdullahi Yakubu Maidoya, ya yi wani zama na musamman da duka shugabannin jam’iyyar na duka ƙananan hukumomi 13 da na gundumomin jihar.

Zaman wanda aka yi a babban sakatariyar jam’iyyar dake garin Lafiya, babban birnin jihar, ya samu goyon bayan duka shugabannin ya kuma samu halarcin wasu jiga-jigan ‘yan jam’iyyar daga ciki da wajen jihar.

Da yake jawabi, Yakubu Maidoya ya gode wa shugabannin jam’iyyar dangane da amsa gayyatar da suka yi duk da an sanar da su a ƙurarren lokaci, ya sanar da su cewa madugun tafiyar jam’iyyar na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne ya umurci a kira taron na musamman don a tattauna dangane da wasu muhimman batuttuwa da suka shafi jam’iyyar tasu.

Waɗanda suka haɗa da jita-jitar nan da jam’iyyar adawa ta PDP ta bakin ɗan takaran ta na shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya yaɗa cewa da shi da Kwankwaso sun kusa cimma yarjejeniyar maja da kuma batun tsare-tsare da kundin manufofin jam’iyyar da sauran su.

Maidoya ya buƙaci shugabannin su yi watsi da jita-jitar don acewarsa lamarin babu gaskiya ciki ko kaɗan.

Ya kuma sanar da su cewa a yanzu bincike ya nuna cewa ba jam’iyyar da ke tsone wa manyan jam’iyyun adawa ido kamar NNPP.

Saboda haka ya kamata su ci gaba da jajircewa don tabbatar da nasarar jam’iyyar a jihar da ƙasa baki ɗaya a lokutan zaɓuɓɓukan da ke tafe.

Ya ƙara da cewa a cikin ƙanƙanin lokaci NNPP ta samu karɓuwa da ɗaukaka a jihar da ƙasa baki ɗaya.

Har ila yau, Maidoya ya bayyana musu wasu daga cikin manufofin jam’iyyar idan suka yi nasara waɗanda suka haɗa da kyawawan tsare-tsare na bunƙasa yankunan karkara da tabbatar da zaman lafiya wadda duka za a yi amfani da su shugabannin ne wajen cimma burin tare da wasu alfanu da za su samu a matsayinsu na shugabannin ciki har da albashi da za su riƙa samu da sauransu.