Buhari ya kira taron Majalisar Ƙasa kan rashin fetur da ƙarancin sabon kuɗi

Daga BASHIR ISAH

Bayanai sun nuna Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya kira taron gaggawa inda zai gana da masu ruwa da tsaki wanda zai gudana ranar Juma’a domin tattauna mafita dangane da matsalar rashin fetur da ƙarancin sabbin kuɗi gabanin babban zaɓe mai zuwa.

Rahoto ya ce, yayin taron wanda za a gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa, ana sa ran Gwamnan CBN ya ba da bayanin halin da ake cike game da sabbin takardun Naira da sauransu.

Kazalika, shi ma Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Mahmood Yakubu da Sufeto Janar na ‘yan sanda, IGP Usman Alƙali Baba, za su yi wa taron bayani game da shirin da suka yi kawo yanzu game da sha’anin zaɓen Shugaban Ƙasa da na ‘yan Majalisar Tarayya wanda zai gudana ran 25 ga Fabrairu, sai kuma na gwamnoni da majalisun jihohi a ranar 11 ga Maris.

Ana sa ran taron zai tattauna muhimman batutuwa yayin da aka tunkari zaɓuɓɓuka masu zuwa domin tabbatar da komai ya gudana cikin nasara da salama.