Kwanan nan matsakaitan ‘yan sandan Nijeriya za su dara, inji Sufeto-Janar

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Sufeton-Janar na ‘Yan Sandan Nijeriya, Usman Alkali Baba, ranar Laraba ya ce duk wani ɗan sanda da ya yi bandaro akan matakin albashi guda ɗaya har na tsawon shekaru biyar tun daga shekarar 2017 yana danƙare za a ciyar da shi gaba nan take.

Babban Sufeton na ‘yan sanda wanda ya nuna damuwar sa da halin lafiya da walwalar ‘yan sanda, ya ƙara da cewar, jami’an ‘yan sanda waɗanda suke matakin mataimakan Sufuritanda zuwa manyan Sufuritanda su ma za su samu tagomashin ciyar da su gaba ko qara masu muƙami.

Da yake yi wa jami’an ‘yan sanda na shiyyar tsaro na bakwai dake Abuja jawabi yayin ziyarar sa wajen ƙaddamar da shirye-shiryen cigaba, Babban Sufeto Baba ya kuma ja hankalin jami’ai da hukumomin tsaro da su riƙa lura da ire-iren mutane da suke yin hulɗa da su.

Ya ce, “lamura na inganta rayuwar jami’ai da walwalar su suna da matuƙar muhimmanci a gare shi. Dukkan jami’an tsaro da suka danƙare a mataki guda na tsawon lokaci tun daga shekarar 2017 za a ciyar da su gaba, ko ƙara masu girma ko muƙami a gobe Alhamis.”

Dangane da gabatowar zaɓen gamagari na ƙasa kuwa, jagoran ‘yan sandan na ƙasa ya bayyana cewar, bada jimawa ba za a horas da jami’ai domin fahimtar da su tanade-tanaden dake cikin dokar zave.

Baba sai ya bayar da umarnin a wadatar da helkwatar shiyyar da motocin gudanar da ayyuka guda biyu, haɗi da na’urori masu ƙwaƙwalwa guda biyu domin inganta ayyukan su na yau da kullum.

Mataimakin Babban Sufeto mai riƙe da shiyya ta bakwai, Mohammed Aliyu ya jinjina wa shugaban nasa bisa yi wa helkwatar shiyyar kwaskwarima.

Ya ce, “dangane da manufar Babban Sufeton na ‘yan sanda bisa bin ƙa’idojin tattali, sanya ido, bin ƙa’idojin doka, kare ‘yancin dan-adam, da haɗin kai da sauran hukumomin tsaro, shugabancin shiyyar yana kamanta aiwatar da abubuwa da suka dace.”

Idan za a iya tunawa dai, Sufeto-Janar ya ƙara wa ƙananan ‘yan sanda kimanin guda 21, 039 girma a watanni uku ko fiye da haka da suka shuɗe, amma har kawo wannan rana ta yau, garin tagomashin bai isa gare su ba.