Mulkin mata zai fi tasiri fiye da na maza – Khadija Iya Abdullahi

“Mata za su iya kawar da matsalolin ƙasar nan idan suka samu dama”

Daga AISHA ASAS 

An daɗe ana kiran sunan mata da babbar murya kan neman na kai da gujewa zaman kashe wando, daɗaɗen jan kunne ne da ya fi gemu tsufa, sai dai har yau wasu matan masu kunnen ƙashi sun sanya ƙafa sun shure wannan shawara ta gyara kayanka, duk da taurin kai na waɗannan mata, bai hana wasu jajirtattun mata ƙara tuna masu ba, kasancewar an ce hannunka ba ya ruɓewa ka yanke ka yar. Hajiya Khadija Iya Abdullahi na ɗaya daga cikin mata masu kishin mata ‘yan’uwansu, kuma tana cikin matan da suka ce sun ji maganar magabata na neman na kai, har ma sun zama wani tsani da mata da kuma matasa har ma da ƙananen yara za su taka don isa ga tudun na tsira.

Masaniyar siyasa ce, kuma ‘yar gwagwarma mai ƙoƙarin ganin am samu canji ta ɓangaren manyan gobe da kuma tallafa wa mata a inda suka gaza. Hakazalika ita ce mamallakiyar shahararriyar mujallar nan ta Turanci wato SI Magazine. A tattaunawar ta da Manhaja, za ku ji irin gudunmawar da take ba wa al’umma ta ɓangaren matasa har ma da siyasar bakiɗaya. Sannunku da jimirin bibiyar jaridar al’umma, Manhaja.

MANHAJA: Mu fara da jin taƙaitaccen tarihinki.
HAJIYA KHADIJAH: To, a takardar haihuwata dai sunana Khadijah Audu Bidda, don shine sunan mahaifina. Ina daga cikin yara na ƙarshe-ƙarshe da haihuwa, amma fa a wurin mahaifina, domin na kasance ‘ya ta farko gun mahaifiyata
.

Mahaifiyata Ni kaɗai ta haifa, bayyan jinkiri mai tsayi, ta inda na samu ɗaya sunana kenan wato Kyautar Allah. Saboda an jima ana nema kafin a same ni. To wannan ne ya yi tasiri ga mutane, kamar yadda aka faɗa min, babbar yayarmu, wadda ita ce ta farko a wurin mahaifinmu, ba ta haihu ba tsayin lokaci, tana nema, amma ba a dace ba, to shine take ganin idan aka ba ta Ni, ta riƙe, za ta iya samun haihuwa, a matsayina na Kyauta. Ina da wata takwas mahaifiyata ta bayar da Ni, riqo na ya koma Iko. Kuma cikin ikon Allah, da ta ɗauke Ni, ba jima wa ta samu cikin ɗanta na farko.

To wannan ne silar komawa ta Iko da zama, a hannunta na yi firamare da kuma fara sakandare. Ina aji biyu a sakandare zama ya sake dawo da Ni gida. A nan na ci gaba da karatu. Shekara biyu haka bayan kammala karatun sakandare na yi aure, ina da shekaru 19 a lokacin, kuma ina da takardar diploma da na na yi a ɓangaren aikin jarida, saboda ƙwarai na ke da sha’awar zama ‘yar jarida.

Bayan auren ne na nemi gurbin karatu a jami’ar Abuja, sai dai ban samu zaɓi na ba, domin ‘Law’ suka ba ni. Da aurena na zama cikakkiyar lauya, ina da cikin ɗana na biyu.

To a rayuwar auren ta ki kin samu albarkar yara nawa?
Waɗanda na haifa da cikina dai su biyar ne, yaran da na riƙe sun kai goma sha biyu, idan aka haɗe da na wa yaran.

Duk da cewa kin yi shuhura a harkar taimakon al’umma, za mu so jin wacce irin sana’a ki ke yi ta karan kan ki ko kuma aiki.
To, zan iya cewa ina cikin harkar taimakon al’umma tsayin lokaci da ya zama Ni na zama shi, duk da haka bayan kammala bautar ƙasa, na yi aiki na tsayin watanni 18 a bankin Aso, wato Aso Savings. To, ganin rashin dacewar sa ga Ni ta wa rayuwa, sai na aje. Sai na fara da taimakon yara, domin na damu matuƙa da goben yaranmu. Sai na tsunduma harkar inganta rayuwar yara. Da kaina na ke zuwa makarantu ina saita alƙiblar yara, ina koyar da su hanyoyin da za su taimaka masu wurin zaɓen rayuwar girma. Daga nan fa sai ya fara haɓaka zuwa gurbi mai zaman kan sa, wanda ake gudanarwa bayan tashi makaranta.

Tasirin wannan aikin da na fara ne ya sa mutane suka fara damuna kan in buɗe gidauniya. A lokacin gaskiya na ƙi, domin a wancan lokacin ina kallon gidauniya a matsayin hanya ta roƙo. Don haka ban buɗe gidauniyar ba ,sai dai na buɗe ‘social enterprise’ da ake kira ‘Beyond meteors limit’. A wannan tafiya ce sai idona ya ƙara budewa, na ga mata ma suna buƙatar irin wannan taimako. To fa daga nan tafiyar ta fara, har na nemo wata ƙawata don mu haɗa ƙarfi da ƙarfe don samar da ingantaccen cigaba. Da yake irin wannan aikin ra’ayi ne, tafiya da ta yi nisa dai ta janye, Ni kuma na ci gaba tun da dai Ni abu ne da na ke sha’awa.

Ina ki ka baro karatun lauya da ki ka yi?
Gaskiya shi karatun lauya tun farko maigidana ne ya sa ni inyi, ba wai ina sha’awar sa ba ne. Kamar yadda na ce a baya, Ni aikin jarida na ke so, a lokacin ma ba sa yi, kuma zaɓi na na biyu ma maigida na je ya sa a canza, saboda shi ya fi son in yi karatun lauya ne. Shi ya sa ma da na kammala, na tataraa takardun na kai ma sa, na ce, ga karatunka nan (dariya). Kuma gaskiya cikin ababen da ya sa na ƙara tsanar karatun, a lokacin da na ke karatun sai na fahimci dokokin ba su dace da mu ba, asali ma ba na mu ba ne, domin ba su dace da irin tamu yanayin halitta ba. Dokoki ne na Turawa. Babu ruhin ɗan Nijeriya a cikin su. Ababen da ake ta kiran demokraɗiyya ba na mu ba ne. Sai na ga me ya sa zan sa kaina a ababen da ban aminta da yanayin tsarinsa ba. Ina ganin ababe da dama da ake yi wanda a na wa kallon na ke ganinsu a matsayin kama da wane. Wannan ta sa ko kotu na je, har barci ke ɗaukata, saboda Ina muhallin da ba na son kasancewa.

Bari in ba ki misali da wasu dokoki kamar na sata, ace sai ka kawo hujja mafi ƙarfi kafin a yanke masa hukunci, ko da kuwa an tabbatar da ya yi. To kinga ba ‘yan Nijeriya ne a cikin dokar ba. Kamata ya yi a a ce dokokin Nijeriya, ‘yan Nijeriya ne suka assasa su. Kuma za mu iya. Idan aka haɗa masana ta kowanne lungu da saƙon Nijeriya za a iya samun dokoki da za mu yi alfahari da su.

Wannan aikin na taimako da kike cikinsa tsayin shekaru goma sha biyar, ya kike samun kuɗaɗen gudanar da shi?
To gaskiya ina samu ne a tsakanin abokai, maigidana, ‘yan’uwa da kuma Ni karan kaina ɗan abin da na ke samu. Daga baya na zo na buɗe mujallar SI, to abin da na ke samu a wannan mujallar na kan tsakuri wani kaso mai nauyi ina aikin da shi.

Kwatsam sai mu ka ji kin faɗa harkar siyasa tsundum, a siyasar ma ba a ƙasa kika soma ba, da takardar Mataimakiyar shugaban ƙasa.
Zan iya cewa wannan wani iko ne na Allah, domin ba abu ne da yake gabana ba kenan. Siyasa shima kamar lauya yake a wurina, sam ba ya cikin ra’ayi na. Ba na son ta, saboda abubuwan da suka lulluɓe ta. Ba wai ta nan Nijeriya ba, kowa ya san siyasa na ko ina ba a tsayawa kan gaskiya kawai, idan sun faɗi magana, suna nufin wani abu daban, don haka ne na ke ganin ko kaɗan bai yi daidai da irin tawa tsarin rayuwa ba. Sai dai kamar yadda na ce rayuwar mutum kaf jarrabawa ce, ba zan manta ba, ina kan gadona, aka kirani, ake sanar da ni, bayyan bincike da dogon nazari kan irin ayyukan da na ke yi, ganin irin taimako da son ƙasa ta da na ke, suke so in zo ayi tafiyar siyasarsu da Ni, don ba da ta wa gudunmawa.

To, daga farko gaskiya ban amince ba, kamar yadda na faɗa, sam harkar siyasa ba ta cikin tsari na. na ce a’a a farko, na sake cewa a’a, kai har sau uku. Sai da aka bi ta wurin maigidana, shine suka yi magana da shi. To fa shine ya tasa ni a gaba. “kina cewa ba za ki yi ba, alhali kina aikin tallafa wa al’umma tsayin waɗannan shekaru, shin bakya tunanin wannan hanya ta siyasa za ta ba ki ƙarfin ƙara taimaka wa mutane.” To fa shi ya bani ƙarfin gwiwa, na ga maganarshi za ta iya kasancewa haka.

To da na shiga siyasar kuma sai na fahimci sanin da na yi wa siyasa. Siyasa tana canzawa. Akwai makarantar da na ke ciki yanzu haka ‘school of politic, policy and good governess’. Makaranta ce da za ta buɗe idonka sosai kan siyasa, a nan na san amfanin siyasa da sauran ababen da suka shafi harkar ɗaukar ragamar al’umma. Na fahimci muna buqatar gyara a sha’ani na irin tafiyar ta mu siyasa. Yana da kyau mu fahimci waɗanda suka dace mu zava don kawo canji ga ƙasarmu, ba wai don abin da za su iya badawa, ko don ƙarfinsu ba. Shi ɗan siyasa ko ince mai muƙami bawa ne na al’umma, idan sun zaɓe shi, zai masu bauta ne na tsayin wani lokaci kafin ya koma inda ya fito. Sai dai har wa yau mun kasa canza akalar siyasarmu, a kullum mutane iri ɗaya muke zava, kuma su zo su kwashe kuɗaɗenmu, kan su da iyalansu kawai suka sani.

Don haka gaskiya ya kamata mu canza kiɗanmu don samun rawar da ta bambanta da baya. Sai fa mun canza yanayin zaɓenmu kafin mu samu canji a yanayin yadda ake mulkar mu. Su kuma shuwagammani su sani, siyasa bai kamata ta zama rigar ado ba da za su sa suna tinƙaho ba, domin Allah zai tambaye su yadda suka tafiyar da mulkinsu.

Ya ki ke kallon Nijeriya a nan gaba ta ɓangaren jinƙai da kuma taɓarɓarewar tarbiyya?
To, idan kika duba ni aikina ya fi tafiya a ɓangaren yara ƙanana da kuma matasa, sannan mata bakiɗaya. Idan za a samu yawaitar masu abin da muke yi, ina da tabbacin za a iya samun sabuwar Nijeriya a matasanmu, domin ba wai muna ba su tallafi ne kawai ba,muna masu tarbiyya, mu karkatar da su kan bin hanyar da zata kai su ga alkhairi. Muna koyar da su yadda za su kula da kan su, kaucewa faɗa wa mugunyar hanyar da za ta kaisu ga lalata rayuwarsu har su fitine al’umma. Don haka idan za mu gyara rayuwar matasa, to tabbas za a samu ingantacciyar Nijeriya a nan gaba.

Hajiya Khadija Iya Abdullahi

A matsayinki ta masaniya kan harkar siyasa, kina ganin za a iya samun canji idan aka ce mata ne ke riƙe da madahun iko manya, kamar shugaban ƙasa da sauransu?
Idan kika duba yanayin yadda Allah ya yi mace, za ki tabbatar idan ta yi mulki za a iya haifar ɗa mai ido. Domin su dama halitarsu ta jagoranta ce. Mace a gidanta, ita ce nauyin duk wanda yake gidan ya rataya wuyanta. Cinsu da shansu kinsan yana wuyanki. Da a ce mace tana cikin kicin, tana dafa aninci, sai a lokacin ta fahimci ba ta da wani abu da take buƙata don abincin ya kammalu, kamar albasa da sauransu. take za ta yi tunanin yadda za ta magance matsalar rashin albasar ba tare da girkin ya samu tasgaro ba. Ma’ana dai tana da baiwa ta magance matsala da namiji ba shi da ita. Abin da na ke ƙoƙarin faɗa shine, mace maganin matsaloli ce, kuma idan ta samu dama, ta tsunduma cikin kogin matsalolin ƙasar nan, ba jimawa za ta kawar da su. Don haka ba za a taɓa ma haɗa iya mulkin mace da namiji ba, domin ita a jininta yake tun tasowarta.

A matsayinki ta mace, waɗanne irin ƙalubale kika samu a tafiyarki ta tallafa wa al’umma?
A gaskiya babbar matsala da na fuskata a wannan tafiya sha’ani ne na kuɗi, muatne na ganin idan kana wannan aikin kana samun kuɗi ne sosai, tallafi daga wurare dabam-daban. To ni gaskiya bana samun tallafi daga irin wuraren da ake tsammani, kamar yadda na faɗa, kuɗaɗen aikin nan yana fita ne a tsakanin ni da iyalaina da kuma wasu abokanai. Sai dai mutane yanzu komai na su zancen kuɗi ne, duk inda za ka je da neman haɗin gwiwa don yin wani abin alkhairi zancen su na kuɗi ne, me za ka ba su, nawa za su tatsa a jikinka.

To mu ji irin nasarorin da ki ka samu?
Wai! Ai nasarorin ne ba za su ƙirgu ba, sai dai a ce Allhamdu lillah. Amma bari inba ki kaɗan, yanzu muna da aƙalla matasa 500 da muka canza wa yanayin tafiyar rayuwarsu, suka nutsu, suka yi watsi da rayuwar da suke yi kafin zuwansu. Kuma har yau muna kan wannan turba. Kaɗan kenan daga ciki.

Daga ƙarshe, wane kira za ki yi ga mata masu zaman kashe wando?
A kullum Ina gaya wa mata, babu mutum da yake a banza, kowa Allah ya ba shi wata baiwa da zai iya sarrafa wa ta zame masa hanyar dogaro da kai. To, ba ki da wata hanyar da za ki kare kanki da ta hanaki neman na kanki. A cikin kowanne halin rayuwa kike, akwai sana’a ko aikin da ya dace da irin taki rayuwar. Ba kya fita, nemi sana’ar da za ki yi a gida, ba ki da jari, yi amfani da ƙarfin jikinki ki samu na kanki, ko ki yi wa wasu aiki su biya ki, ko ki amso na wasu su na biyan ki. Don haka mata ku nemi abin da za ku rufa wa kanku asiri, ku fitar da kanku daga layin ’yan roƙo, waɗanda ba su san komai ba sai gulma da tsugudidi, domin duk inda zaman banza ya samu gindin zama, to fa sai dai ka tarar ya ba wa gulma, sa ido da munafurci wurin zama.

Madalla. Mun gode.
Ni ma na gode ƙwarai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *