Kyan alƙawari cikawa

Daga Lubabatu Lei

Daga ranar 13 zuwa 15 ga wata, an gudanar da taron kolin kasar Amurka da kasashen Afirka karo na biyu a birnin Washington, babban birnin kasar ta Amurka, wato shekaru 8 ke nan tun bayan da aka gudanar da taron a karo na farko.

A shekarar 2014, gwamnatin Obama ta gudanar da taron karo na farko, inda kuma ya yi alkawarin karfafa huldar da ke tsakanin kasar Amurka da kasashen Afirka da ma gudanar da taron a kai a kai. Sai dai ba a yi zaton za a jima tsawon shekaru 8 kafin a kaddamar da taron a karo na biyu ba.

Kwana daya kafin a bude taron na wannan karo, Amurka ta lashi takobin samar da dala biliyan 55 cikin shekaru uku masu zuwa, don tallafa wa kasashen Afirka ta fannonin tattalin arziki da kiwon lafiya da tsaro da sauransu. Daga bisani, ta kuma sanar da habaka kawancenta na binciken sararin samaniya don shigar da wasu kasashen Afirka a ciki, baya ga kuma bayyana goyon bayanta ga shigar da kungiyar tarayyar Afirka cikin kungiyar G20.

Babu shakka, abubuwan alheri ne ga kasashen Afirka. Amma ana nuna shakku a kan alkawuran, sakamakon yadda gwamnatin Amurka ta kasa cika alkawuran da ta dauka a gun taron da aka gudanar karo na farko a shekarar 2014. A lokacin, gwamnatin Amurka ta dauki alkawura da dama, amma ga shi bayan taron, a maimakon ta cika su sai ta rage kudaden jarin da ta zuba wajen yaki da cutar kanjamau a Afirka, tare da rage gudummawar da ta samar a shiyyar. Idan ba a manta ba kuma, gwamnatin Amurkar ta sanar da jerin shirye-shirye na tallafi, ciki har da “samar da lantarki a Afirka”, wanda ya yi alkawarin samar da wutar lantarki da suka kai MW dubu 20 ga kasashen Afirka ya zuwa shekarar 2020, amma kawo karshen shekarar 2020, lantarkin da aka samar bai kai kaso 1/4 na abin da ta alkawarta ba. Sabo da haka, idan gwamnatin Biden na son sake samun imani daga kasashen Afirka, dole sai ta cika alkawuran da aka dauka a baya tukuna.

Mene ne dalilin da ya sa Amurka ke son daukar alkawura amma ba tare da cikawa ba a gaban kasashen Afirka? In mun yi nazari, za mu ga cewa ainihin abin da ya sa take bunkasa alakarta da kasashen Afirka shi ne don su taimaka wajen ja-in-ja da take da wasu manyan kasashe, a maimakon a ce ta mai da su abokan hadin gwiwa na zaman daidaito da kuma cin moriyar juna, ballantana ta mai da hankali a kan daidaita matsalolin da ke ci musu tuwo a kwarya.

Wasu kafofin yada labarai na kasashen yamma sun ce, a gun taron na wannan karo, jami’an kasar Amurka sun mayar da hankali sosai wajen ganin bakin na Afirka, ba su ji kamar ana matsa musu su yi zabi tsakanin “mu ko su” ba. Amma furucin da ministan tsaron kasar Lloyd Austin ya yi a wajen taron, ya tona mana ainihin abin da take neman cimmawa, inda ya ce, a yayin da Sin da Rasha ke kara taka rawa a harkokin nahiyar Afirka, kasashen biyu ka iya “lalata kwanciyar hankalin nahiyar”.

To, kasashen Afirka sun san wane ne aminansu na gaskiya, haka kuma suna sane da abin da Amurka ke neman cimmawa. Don kafin taron, shahararriyar cibiyar nazarin manufofin diplomasiyya ta kasar Afirka ta kudu da aka san ta da sunan “The Institute for Global Dialogue of South Africa” ta fitar da rahoton cewa, ita kanta Amurka ce ke amfana da manufofin da ta samar kan Afirka, kuma ta gaza cika alkawuran da ta dauka, wadda take neman karfafa babakere a nahiyar Afirka da sunan dimokuradiyya. Rahoton ya kuma bayyana cewa, kwatankwacin yadda Amurka ke son kafa babakere da ma ba da lacca, kasar Sin ta fi samun karbuwa a kasashen Afirka sakamakon irin matsayinta na rashin tsoma baki cikin harkokin gida da ma samun moriyar juna a yayin da take hulda da kasashen Afirka.

A yayin da ake fuskantar munanan tasirin annobar Covid-19 da rikicin Rasha da Ukraine da ma sauyin yanayin duniya ke haifarwa ga tattalin arziki da zaman al’umma, kasashen Afirka na matukar son ganin a samar musu tallafi da gudummawa wajen fuskantar matsalar karancin abinci da ta tattalin arziki, kuma a hakika, Amurka na iya samar da taimakonta. Kasar Sin a nata bangaren na son ganin karin kasashen da suka hada da Amurka sun ba da gudummawarsu ga Afirka, haka kuma tana fatan Amurka za ta dauki hadin gwiwarta da kasashen Afirka yadda ya kamata. Daidai kamar yadda jakadan kasar Sin a Amurka mista Qin Gang ya bayyana a kwanan baya cewa, “Ya kamata nahiyar Afirka ta kasance dandalin hadin gwiwar kasa da kasa, a maimakon fagen takara a tsakaninsu.”

Mai fassara: Lubabatu