Labaran ƙarya na barazana ga ‘yancin faɗin albarkacin baki – Ahmed Maiyaki

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Babban Jami’in Yaɗa Labarai na Cigaban Ƙungiyar Fafutukar Neman ’Yancin ’Yan Jarida, Malam Ahmed Maiyaki, ya bayyana damuwarsa kan ƙalubalen da ake fuskanta na ’yancin aikin jarida a kasar nan.

Maiyaki ya bayyana “labarai na ƙarya” da kuma bayanan ƙarya a matsayin wani ɓangare da ke barazana ga ‘yancin faɗin albarkacin baki a matsayin kan gaba ga sauran ‘yancin ɗan adam.

Shugaban na MDINIGERIA a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a Kaduna a ranar Larabar da ta gabata ya bayyana cewa, taken ranar ’yan jarida ta duniya ta 2023: ‘Shaping a Future of Rights: Freedom expression as a driver for all other human rights,’ ba wai kawai koyarwa ba ce, amma wani al’amari ne da ke kan gaba kamar yadda yake nuna ikon ‘yancin faɗar albarkacin baki don morewa da kare duk wasu haƙƙoƙin ɗan adam.

“Ko da yake matsayin ‘yan jaridu na duniya yana da muhimmanci wajen samar da manufofin dimokuraɗiyya da ‘yancin yaxa labarai. labaran ƙarya sun zama babbar barazana ga ‘yancin faɗin albarkacin baki, aikin yaɗa labarai da dimokraɗiyya mai ɗorewa,” in ji shi.

Maiyaki ya kuma gargaɗi masu aikin yaɗa labarai da su yi taka-tsan-tsan da madogararsu ta hanyar tantance gaskiya domin tabbatar da sahihanci da kaucewa rikice-rikice.

A cewarsa, yayin da duniya baki ɗaya ta damu da irin haɗurran da ’yan jarida ke fuskanta wajen gudanar da ayyukansu, dole ne kuma mu damu da yadda qwararru ke gudanar da ayyukansu wajen tsara makomar ’yancinsu ta hanyar ɗa’a da aikin jarida.

Ya ƙara da cewa, “Dole ne ‘yan jarida su kasance masu bin doka da kuma kare muradun jama’a ta hanyar tattara sahihan bayanai da yaɗa labarai da ke tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali; a matsayin wani mataki na inganta ’yancin faɗin albarkacin baki.”

labaran ƙarya na barazana ga ‘yancin faɗin albarkacin baki – ahmed maiyaki

daga mahdi m. muhammad

babban jami’in yaɗa labarai na cigaban ƙungiyar fafutukar neman ’yancin ’yan jarida, malam ahmed maiyaki, ya bayyana damuwarsa kan ƙalubalen da ake fuskanta na ’yancin aikin jarida a ƙasar nan.

maiyaki ya bayyana “labarai na ƙarya” da kuma bayanan ƙarya a matsayin wani vangare da ke barazana ga ‘yancin faɗin albarkacin baki a matsayin kan gaba ga sauran ‘yancin ɗan adam.

shugaban na mdinigeria a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a kaduna a ranar larabar da ta gabata ya bayyana cewa, taken ranar ’yan jarida ta duniya ta 2023: ‘shaping a future of rights: freedom expression as a driver for all other human rights,’ ba wai kawai koyarwa ba ce, amma wani al’amari ne da ke kan gaba kamar yadda yake nuna ikon ‘yancin faɗar albarkacin baki don morewa da kare duk wasu haƙƙoƙin ɗan adam.

“ko da yake matsayin ‘yan jaridu na duniya yana da muhimmanci wajen samar da manufofin dimokuraɗiyya da ‘yancin yaɗa labarai. labaran ƙarya sun zama babbar barazana ga ‘yancin faɗin albarkacin baki, aikin yaɗa labarai da dimokraɗiyya mai ɗorewa,” in ji shi.

maiyaki ya kuma gargaɗi masu aikin yaɗa labarai da su yi taka-tsan-tsan da madogararsu ta hanyar tantance gaskiya domin tabbatar da sahihanci da kaucewa rikice-rikice.

a cewarsa, yayin da duniya baki ɗaya ta damu da irin haɗurran da ’yan jarida ke fuskanta wajen gudanar da ayyukansu, dole ne kuma mu damu da yadda ƙwararru ke gudanar da ayyukansu wajen tsara makomar ’yancinsu ta hanyar ɗa’a da aikin jarida.

ya qara da cewa, “dole ne ‘yan jarida su kasance masu bin doka da kuma kare muradun jama’a ta hanyar tattara sahihan bayanai da yaɗa labarai da ke tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali; a matsayin wani mataki na inganta ’yancin faɗin albarkacin baki.”