Mahaifi ya kai ɗansa kotu domin ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai-da-rai a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wani fusataccen mahaifi ya yi karar dan cikinsa a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Fagge ’Yan Alluna a Jihar Kano.

Mahaifin ya koka da cewa ɗan nasa ya addabe shi da sace-sace da kuma shaye-shaye.

Mahaifin, wanda aka ɓoye sunansa ya nemi kotun ta ɗaure ɗan nasa har illah ma sha Allah.

Mai gabatar da ƙara, Abdul Wada, ya karanta wa wanda ake ƙarar tuhume-tuhumen da ake masa, inda nan take ya amsa laifinsa.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Malam Umar l Lawan Abubakar, ya ɗage sauraren shari’ar zuwa ranar 6 ga watan Yuni 2024 don yanke hukunci.