Mai juna biyu ta datse mazaƙutar mijinta da wuƙa a Taraba

Wata matar aure mai shekara 25 ta datse mazaƙutar mijinta a garin Tella da ke ƙaramar hukumar Gassol na Jihar Taraba.

Matar mai suna, Halima ta tafka wannan aika-aikar ne a ranar Talata yayin da mijinta, Umar Aliyu ke sharar barci.

Ƙanin wanda abin ya faru da shi, Shagari Umar, ya ce, ihun Aliyu ne ya jawo hankulan mutane inda suka zo suka tarar da shi kwance cikin jini.

Umar ya yi ikirarin cewa, “mun ga matarsa Halima zaune a gefen gado riƙe da wuƙar da ta yi amfani da shi wurin datse mazaƙutar ɗan uwanmu.

Ya ƙara da cewa, ƙiris ya rage fusattaun ’yan uwan Umar da maƙwabta su yi mata duka, amma manya sun shiga tsakani sun ce a tausaya mata saboda tana ɗauke da juna biyu kuma suka kira ’yan sanda.

A cewarsa, an garzaya da Aliyu zuwa Cibiyar Lafiya ta Tarayya, FMC, da ke Jalingo mai nisar kilomita 150 daga garin Tella.

Ya ce, da isarsu asibitin, an bawa Aliyu kulawa cikin gaggawa aka tsayar da jinin da ke zuba daga raunin bayan an masa tiyata.

Likitan da ya kula da Aliyu, Dakta Kyantiki Peter Adamu, ya shaida wa manema labarai cewa, an kira shi sashin waɗanda ke buƙatar kula cikin gaggawa don wani majinyaci da aka kawo bayan datse masa mazaƙuta.

“Abinda muka yi shine tsayar da zubar jinin cikin gaggawa da kuma yi masa tiyata a inda aka masa rauni saboda ya rasa jini sosai kafin a kawo shi,” inji shi.

Ya ce, bisa ga dukkan alamu majinyacin zai murmure, amma ’yan uwansa sun buƙaci su tafi da shi saboda haka babu abinda asibitin zai yi a kai.

Shagari ya shaida wa manema labarai cewa, sun ɗauke Aliyu daga FMC Jalingo ne domin su tafi da shi wani asibiti a Gombe.

Mun ɗauke ɗan uwan mu daga FMC Jalingo mun tafi da shi FMC Gombe domin ya ƙara samun kulawar da ya ke buƙata, inji Shagari.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP David Misal ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya ƙara da cewa, ’yan sanda sun kama Halima sun kuma fara binciken dalilin faruwar lamarin.