Me yake kawo zargi a zaman aure?

Barkanmu da sake haɗuwa a wani makon a shafinku na Zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. A wannan mako kuma muna tafe da matsalar zargi a zaman aure. Wannan matsala ta zama ruwan dare a cikin gidajen aure.

Mene ne zargi?

Da farko dai zargi yana nufin zaton wani abu yana faruwa ko zai faru ko kuma ya riga ya faru wanda kuma babu tabbaci a ciki. Kawai zuciyar mutum za ta dinga yi masa saƙe-saƙe da wasi-wasi na akwai wasu abubuwa da suke faruwa ko ya gane meye shi ko bai gane ba.

Kuma ko yana da hujja ko ba shi da ita. A wajen mai zargi, ko yaya abu yake, zai iya sa shi ya fara jin wasi-wasi a zuciyarsa ya afka gonar zargi.

Meye yake jawo zargi a tsakanin ma’aurata?

Akwai daililai da yawa da suke kawo zargi a tsakanin ma’aurata a gidan aure. Kuma zargi ba ƙaramin rushe gidan aure yake yi ba. Domin shi aure da ma ana gina shi ne bisa yarda da amincewa tsakanin mutum biyu.

Duk auren da rashin yarda ya shigo ciki, da wuya ya yi tsahon kwana. Ko a musulunce zargi yana haramta aure. Amma idan zargi ya riga ya fara shiga tsakanin ma’aurata, shikenan kuma an dinga kenan.

Shaiɗan ya riga ya yi katutu a gida, sai ta Allah kuma. Wasu daga cikin abubuwan da suke jawo zargi a gidan aure sun haɗa da:

*Tsoron abinda ya faru a baya: Hausawa dai sun ce wai: “Idan maciji ya sare ka, idan ka ga baƙin tsumma ma sai ka gudu”. Allah ya halicci Ɗan Adam da ɗabi’ar tsoron abinda ya same shi a baya, ya maimaita kansa.

Don haka, idan namiji ko mace suka sha wahala a kan aure, ko aka yaudare su ko aka ha’ince su a aure ba tare da sun farga ba, za su kasance masu taka-tsan-tsan da gudun faruwar abun a gaba. To a garin kaffa-kaffa kuma sai su fara zargi.

Misali, namijin da ya taba soyayya ko auren mace mai neman maza ko sata, ko wata ɗabi’a, kawai a wajensa duk mata haka suke. Sai wacce ya jarraba ta cinye jarrabawar kaɗai ce zai iya warewa daga cikin zarginsa. Don haka kowacce mace abar zargi ce a wajensa. Ko ta yi abin zargin kuma ko ba ta yi ba, ‘yanuwanta mata sun jawo mata. Haka abin yake a wajen mace ma.

Kullum za ta yi ta kula da takun wannan mijin da ta aura don zargin zai iya ha’intarta kamar yadda miji ko saurayinta na baya ya sha ta basulla. Haka ko a kan wani makusancinsu abu ya faru, shi ma dai sammakal. Zai sa su shiga kiyaye yadda abin ba zai faru a kansu ba.

Ta hanyar kula da sa ido da kula da duk wani abokin zamansu. Ko kuma shi abokin zaman yana da wata ɗabi’a a baya amma yanzu ya tuba. Hakan zai sa shi ma a dinga zarginsa ko zai koma ruwa. Shi ma wannan yana kawo hatsaniya.

*Rashin yarda da kai da ƙimanta kai: Mace ko namiji idan ba su yarda da kansu ba, yana sa tsarguwa a zuciyarsu. Ka yi ta tunanin aboki ko abokiyar zamanka suna ha’intarka ko sun raina ka.

Wannan yana faruwa ne saboda rashin zuciya mai kyau da kuma rashin bar wa Allah komai. Kuma zargi ba abinda yake kawo wa sai zunubi. Domin musulunci ya ce, zato zunubi ne, ko da kasance gaskiya. Allah ya kiyashe mu.

*Rashin kauna: Rashin ƙauna yana sa mutum ya ji kullum a cikin dakon laifin wani yake. Idan mace ba ta son namiji kullum a cikin dakonsa take yi don ya yi laifi.

Don haka duk wani motsinsa tana zargin wani mugun abin yake shiryawa. Haka namiji ma idan ba ya ƙaunar mace kullum Allah-Allah yake ya kama ta da wani laifi don ya zame masa hujja a gare ta. Ko ya rabu da ita ko ya hukuntata ta. Shi dai ƙuntata shi ne fatansa. Shi ya sa ake son ka auri ko ki auri waɗanda kuke so.

Domin ko ba ku ƙulla auren gabaɗaya kan soyayya ba, a qalla akwai soyayyar da za ta sa ku dinga yi wa junanku uzuri. Idan da so da uzuri kuma, zargi bai fiye samun gindin zama ba.

*Tsegumi/zuga: A kullum munafukai suna daɗa ƙara bunƙasa don ganin sun tarwatsa gidan aure. Sauraren mazuga da magulmata da ma’aurata ke yi kan iya kai wa ga suna zargin juna.

Musamman ma idan ba ku tsaya kun buɗe zuciyarku kun fahimci abokan rayuwarku ba, gulmammakin sai su yi tasiri. Musamman ma kuma idan an gaya muku zancen ba ku je kun tattauna da abokin rayuwarku ba. Sai ku riqe su a zuciyarku, ku yi ta kallonsa da abun. Har ma duk wani motsi da ya yi ko na alkhairi ne, sai shaiɗan ya dinga yi muku wasi-wasin anya kuwa ba wancan labarin da kika ji ba ne yake ƙara tabbata?

Don haka, hattara da mazuga. Ko da ‘yanuwanku ne na jini ko aminanku. Kowa zai iya yin ƙarya. Abubuwa da yawa da za a faɗa ƙarya ne. Amma rashin gogewa ya kasa sa ku gane haka.

*Rashin fahimtar juna: Rashin fahimtar juna na kawo jahiltar manufar abokin rayuwa. Sai a yi ta zargin juna a kan igiyar zato kawai. Wato a kan abinda ba a fahimce shi a kai ba.

*Aikata mugayen ayyuka a ɓoye: Idan ɗaya daga cikin ma’aurata yana aikata mugayen ayyuka a ɓoye kuma ba tare da asirinsa ya tonu ba, to gani suke shi ma abokin zamansu yana aikatawa kawai asirinsa ne bai tonu ba.

Abubuwa musamman zina tana ɗaya daga cikin abubuwan da suke jawo wannan zargin. Idan kuka lura, namiji mai neman mata ya fi kowa zargin matarsa, da yi mata kulle da hana ta mu’amala har da ‘yanuwanta na jini.

Gani yake ko tsakaninta da danginta shaiɗan zai iya ribatarsu. Sannan mace ma za ta iya yin wannan zargin saboda tana aikata abu. Masu wannan hali suna da tsananin zargi da kishin abokan zamansu.

*Zurfafa bincike tsakanin ma’aurata: Ko musulunci ya ce, A daina zurfafa bincike don a zauna lafiya. Bahaushe ya ce, kaza garin tone-tone take tono wuƙar yanka ta. Ma’ana, in dai mutum zai ta bincike, watarana zai binciko abinda ba zai masa daɗi ba.

Don haka, son binciken ƙwaƙƙwafi a kan abokin zama ba abinda yake jawo wa sai a gano abubuwan tashin hankali ma waɗanda wasu sun fi ƙarfin magancewarku. Misali, kamar mace mai binciken wayar miji za ta iya ganin abinda zai iya tayar mata da hankali ta afka duniyar zargi ba dare ba rana.

Kuma jin daɗin Duniya ya ƙaurace mata. Wata kuma har shafukansa na Wasaf da Fesbuk shiga take ta ga wainar da yake toyawa. Wata ba yammata ba, har kishiyarta sai ta binciki irin hirar da suke da miji. Wani mijin kuma har lave yake yi wa matarsa idan tana waya da iyaye ko ‘yanuwa.

Shi kansa binciken a musulunce haramun ne. Kuma dole daga ƙarshe kuma a fara zaman tashin hankali idan da ƙarar kwana, aure ya watse.

Halittar zargi: Wasu kuma haka Allah ya yo su da halittar zargi. Ko tare da wasu mutane suke kullum tunaninsu zancensu ake, ko cutarsu ake so a yi. Ina ga kuma mata ko mijinsu na aure?

To haka za su kasance kullum cikin zargin aboki ko abokiyar rayuwarsu. Irin waɗannan mutane abin tausayi ne. Don ba ƙaramar lalura ba ce. Shaiɗan ba ya son su zauna lafiya kullum a cikin sa su shakku yake a kan mutane. Saboda haka, kullum a cikin zargi yake.

Irin waɗannan mutane sai dai a yi haƙuri a zauna da su, ba don halinsu ba. Don idan aka biye wa halinsu, har iyayensu da ‘yanuwansu ba za su zauna da su ba. Domin su da abinda suke so da wanda ba sa duk zargi ne.

*Kishi mai tsanani: Idan Allah ya halicci mutum da kishi mai tsanani shi ma yana cikin tashi hankali. Domin baƙƙin kishi babbar lalura ce wacce take iya sanya mutum a cikin zargin mai tsanani a kan dukkan wanda yake so.

Domin zai kasance mai tsananin ƙulafuci ga wanda yake ƙauna har ya dinga tsoron ma kada wani abu ko wani mutum ya rave shi ko ita. A dalilin haka, irin mutanen nan suke da tsananin zargi a kan abokan rayuwarsu ta aure. Duk wani motsi idonsu yana kai yake. Duk wanda mata ko mijinsu ke mu’amala da shi, abin bin zargi ne.

Wani har ‘yanuwanta na jini ma kishi yake da su. Kun ga maganata ta dawo ta cewa baƙin kishi lalura ce babba. Sai ka ga ana ta tashin hankali saboda wanda ake zargin zai kasance cikin rashin jin daɗi kuma tun ba ya magana har ya yi.

Misali akwai matan da idan suka ga lambar mace a wayar mijinta dole sai su ce nemanta yake yi. Shi kuma zai ga yaya za a yi masa ƙazafi? Ba sai na gaya muku dai me zai biyo baya ba.

*Buɗe ƙofar zargi: Wasu kuma ba haka kawai ake zargin su ba. Su ne suke bayar da ƙofar zargin da kansu. Wasu matan basu da kamun kai ga kule-kelen maza da shigar banza. Ba ƙaramin danne zuciya namiji zai yi ba ya ƙi zargin su.

Haka rashin dawowa gida da wuri (a dinga haura lokacin da aka saba dawowa daga nema, ko wani waje). Ko liƙe wa waya da sa mata lambobin sirri, ko waya a asirce don kada abokin zama ya ji, da sauransu. Ko kuma mutum ya canza daga halayyar da aka san shi da ita.

Misali, lokaci guda abokin zama ya janye kulawarsa ga abokin zama. Ko miji ya daina mu’amalar aure da matarsa. Ko kuma haka kawai namiji ya daina wadata iyalinsa yadda ya saba Dole za a dasa ayar tambaya a kan ire-iren abubuwan nan.

Za mu cigaba a wani makon idan rai ya kai. Za mu ƙara muku da illar zargi a tsakanin ma’aurata da kuma hanyoyin da za a kawar da su.

Ina godiya sosai ga masu kiran waya don yin tsokaci ko fatan alkhairi. Makarantana kullum kuna raina. Allah ya saka da alkhairi.