Ya halaka matarsa saboda ta shanye masa koko

Wani matashi a Jihar Neja ya halaka matarsa har lahira saboda rikicin da ya ɓalle tsakaninsu saboda koko.

Lamarin ya faru ne a Ƙauyen Kadaura da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Rafi da ke jihar.

An samu bayanai akan yadda ya fara da lakaɗa ma ta duka kawo wuƙa wanda ya yi sanadiyyar mutuwarta.

Wani matashi mai shekaru 20 ya halaka matarsa bisa rikicin da su ka samu saboda Koko kamar yadda majiyoyi su ka tabbata.

An samu labarin yadda lamarin ya faru a ƙauyen Kadaura da ke ƙaramar hukumar Rafi, inda matar ta rasa ranta bayan mijinta ya zane ta.

Bayan cin bakin dukan ne ta kwanta rai a hannun Allah wanda daga bisani ta rasa ranta.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya bayyana cewa, “wanda ake zargi ya riga ya amsa laifinsa inda ya ce, ƙaramin saɓani su ka samu tsakaninsa da matarsa saboda koko wanda hakan ya sa ya dake ta.

“Take anan ta faɗi rashe-rashe wanda aka zarce da ita asibitin Wushishi rai a hannun Allah daga nan likitoci su ka tabbatar ta rasu.”

Kakakin rundunar ’yan sanda ya bayyana wa manema labarai cewa, yanzu haka matashin yana hannun ’yan sanda a babban ofishinsu da ke Kagara yana amsa tambayoyi.

A cewar Abiodun, bincike ya kammala kuma za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.