Majalisa za ta binciki sojojin ruwa bisa ƙone jirgin da suka kama da ɗanyen man sata

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar Wakilai ta yanke shawarar bincikar jami’an Rundunar Sojojin Ruwa bisa zargin su da bankawa tare da ƙone jirgin ruwan da suka kama maƙare da ɗanyen man Nijeriya na sata.

Hakan ya biyo bayan amincewa da ƙudirin gaggawa kan muhimmancin qasa da ɗan majalisar wakilai Onofiok Luke (PDP- Akwa-Ibom) ya gabatar a zaman majalisar da aka yi ranar Laraba a Abuja.

Taken ƙudirin nasa shi ne: ‘Akwai buƙatar a gaggauta gudanar da bincike kan yadda aka ƙona jirgin mai da ake zargin jami’an tsaro na da hannu wajen satar mai’.

Hon. Luke ya gabatar da cewa matsalar satar man fetur matsala ce da ta daɗe a yankin Neja-Delta kuma ta haifar da mummunar lalacewar muhalli a yankin.

Ya ce hakan ma ya yi illa ga samar da kuɗaɗen shiga na Nijeriya wanda ya sa ƙasar ta yi asarar gangar ɗanyen mai 470,000 a kowace rana wanda ya kai Dala miliyan 700 duk wata.

Ya ce ƙiyasin da NNPC ta yi ke nan, kuma an samu rahotanni da dama cewa an yi amfani da fasahar zamani wajen satar ɗanyen mai.

Ya ba da misali da bututun da aka gano ba bisa ƙa’ida ba a baya-bayan nan mai tsawon kilomita huɗu da ya tashi daga tashar mai na Forcados zuwa cikin teku da kusan ganga 200 na ɗanyen mai da aka ce ana satar a kullum tun daga shekarar 2014.

A cewarsa, martanin da kamfanin tsaro mai zaman kansa, Tantita Security Services ya yi wajen daƙile satar mai ya sa aka kama wani jirgin ruwan farautar mai ba bisa ƙa’ida ba tare da miƙa shi ga hukumar tsaro.

Luka ya bayyana damuwarsa game da yadda jami’an tsaro suka ce sun lalata jirgin a maimakon yin amfani da shaida iri ɗaya don gabatar da ƙara.

Majalisar ta yanke shawarar yin gaggawar gudanar da bincike kan lalata jirgin da jami’an tsaro suka yi a maimakon ajiye shi a matsayin shaidar kotu.