Majalisar Dattawa ta sahale wa Tinubu tsige wasu manyan jami’ansa

Daga BASHIR ISAH

Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar mata ta neman tsige Mataimakin Babban Jami’in Hukumar FCCPC, Barrister Babatunde Irukera.

Wasiƙar da Tinubun ya aike wa Majalisar wadda Shugaban Majalisar ya karanto ta yayin zaman Majalisar a ranar Laraba, ta nuna Tinubu ya buƙaci tsige Irukera ne saboda rashin kataɓus.

Dokar FCCPC ta tanadi cewa, sai da sahalewar Majalisar Dattawa kafin Shugaban Ƙasa zai iya tsige Mataimakin Babban Jami’in Hukumar.

Sanarwar da ta nuna tsige Irukera ta sake nuni da yadda Tinubu ya tsige Babban Daraktan hukumar Bureau of Public Enterprises (BPE), Alex Okoh, tare da sanar da waɗanda za su maye guraben waɗanda tsigewar ta shafa.

Bayan tafka zazzafar muhawara kan wasiƙar a zauren Majalisar, daga bisani Shugaban Majalisar, Sanata Apkabio ya ba da damar kaɗa ƙuri’ar jin ra’ayi wanda a ƙarshe waɗanda suka goyi bayan wasiƙar suka yi rinjaye.