A da neman albarkar aure ya fi yawa a zukatan mutane fiye da yawan lefe – Saliha Zariya

*Lefe yana da kyau, muddin aka karve shi a yadda ya zo – Fatima Ɗanborno

Daga AISHA ASAS

Kamar yadda muka sani, shafin Gimbiya shafi ne na musamman da ke faɗakar da mata ta ɓangarori da dama, tare kuma da bayyana haƙoƙƙinsu da kuma ilimitar da su kan abinda ya shafi rayuwarsu da kuma zamantakewar aure.

Don haka ne ma shafin bai tsaya a iya fira da mata don jin rayuwarsu da hanyoyin da suka bi don samun cigaba tare da ƙalubalen da suka fuskanta don ya zama wata makaranta ga sauran mata ba, domin mukan zaƙulo muhimman ababe ko matsaloli, mu yi bajikolin su a wannan shafin, don samun mafita, ko lurarwa ga mata masu bibiyarmu.

A wannan makon, za mu tattauna da taurarin mata guda biyu, da suka jima suna bayar da gudunmuwa a faɗakar da mata kan sha’anin gyara kayanka, inda za mu tattauna lefe da tasirin sa a Ƙasar Hausa. Don haka idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da Saliha Abubakar Abdullahi Zariya da kuma Fatima Ibrahim Garba Ɗanborno:

MANHAJA: Barkanku da zuwa wannan fage na tattauna sha’anin da ya jivince mata a ƙarƙashin shafin Gimbiya na jaridar Blueprint Manhaja.

HAJIYA SALIHA: Assalamu alaikum wa rahmatullah. ‘Yan uwa barkanmu da wannan lokacin, ina farin cikin kasancewar tare da waɗannan hazikan taurari da nike jinjina ayyukansu na rubuce-rubuce da fatan Allah Ya ƙara hikima da jagorancinsa gare mu dukka.

FATIMA ƊANBORNO: Assalamu alaikum. Barkanmu da wannan lokaci. Haƙiƙa na ji daɗin kasancewa a cikin wannan dandali da yake magana akan lefe.

Darasin mu na wannan mako shi ne, tasirin lefe a Ƙasar Hausa. Don haka zan soma da tambaya ta farko ga Hajiya Saliha Abubakar Abdullahi Zariya. Ko za mu iya jin wani abu na daga yadda aka samar da yin lefe a Ƙasar Hausa?

Lefe wasu kaya ne da Ƙabilar Hausawa suka assasa ko in ce al’ada ce da ta samo usuli daga Ƙasar Hausa ta kuma jivanci wasu ƙabilun irin Fulani, Kanuri, Bare-bari, Shuwa da ma sauran wasu ƙabilun da ke daraja irin wannan al’ada, a inda ango ke siyan sabbin tufafi da sauran kayan kwalliya tare da gudunmuwar dangi, a haɗa, a kai wa amarya duk da hakan bai nufin ɗauke nauyin tufatarwa da ya rataya kan mijin wanda addinin Islama ya koyar.

A zamanin dauri ana yin kayan lefe ne domin mutuntawa da girmama amarya kasancewarta sabuwa ba don wani burgewa ko abin alfahari ba. Amfaninsa a kan ɗauki lokaci ango bai yiwa amaryarsa kaya ba.

A zamanin da ya gabata ana zuba kayan lefe a cikin wata jaka ce da ake saƙawa da kaba, sai aka koma jakar fata, sai fanteka ko kwanon kaya, daga nan sai aka ci ga gaba ana zubawa a kwalla ko kumbo kafin zamani ya taho da fantimoti, sai kuma akwatuna masu taya.

Kuma saboda muhimmancin wannan al’adar ce ya sa kusan kashi 99.99% na angwaye sai sun haɗa wannan kayan lefe sun kaiwa amare.

Sis Fatima Ibrahim Garba Ɗanborno, wane irin matsayi za ki ba wa lefe a aure?

A taƙaice kamar yadda da yawanmu muka sani yin kayan lefe wata daɗaɗɗiyar al’ada ce da muka taso tun kaka da kakanni a cikinta. Amaimakon mu yi ƙoƙari wurin taƙaita yadda lefen zai kasance, sai muka ɗauki wannan al’ada muka mayar da ita dole.

Shi dai lefe ana yinsa ne domin a farantawa amarya da iyayenta. Wasu da dama kuma suna yinsa ne, domin su nunawa duniyar ƙarfin arzikinsu, ko kuma domin alfaharin ‘yar wance bata sami kamar nawa ba.

Ba mata ne kaɗai suke gasa a lokacin lefe ba, hatta mazan da gidajen mazan suna da irin wannan gasar.

Idan ɗan kishiya ya yi akwatina biyar, insha Allahu idan ɗan amarya ya tashi aure sai a fara tunanin yadda za ayi ace akwatunan ɗan amarya ya fi yawa.


Ni gaskiya a nawa ra’ayin akan lefe kai tsaye zan iya cewa bai zama dole ba, idan kuma har za a yi ɗin, kada ayi la’akari da me aka kawowa wancan.

Gaba ɗaya fa a wannan zamanin, tunda akan zamanin muke magana, bari mu tafi kai tsaye halin da ake ciki akan lefe. Wallahi muddin ba mu cire ƙarya ba, ba zamu taɓa ganin daidai a komai namu ba.

Ko da lefe ko babu laifi, haƙƙin ango ne ya ciyar da matarsa, ya tufatar da ita, ya kuma kula da lafiyarta.

Ban ce kada ayi lefe ba, amma idan aka cire ƙarya, za a sauƙaƙawa ango, haka shima kuma dole ya cire zuciyarsa da ga kan wasu abubuwa na ɓangaren amarya.

lefe ba dole ba ne, amma zai taimaka kwarai! Mece ce ƙaryar da nake so a cire?

Idan aka yi rashin dace da gidan da amarya ta fito, za ku ga ankawo kayan lefe iyayen amarya suna ɗagawa suna yamutsa fuska. Har hakan ya kai matsayin da iyayen angon za su ji babu daɗi a zuciyarsu.

Daga nan sai wasu rigingimu su shigo ciki. Iyayen ango su koma suna cewa an yi masu wulaƙanci. Daga nan amarya zata canza fuska saboda an yi mata fomfo akan lallai kada ta yarda. Tayaya zai saka mata ƙananun zannuwa a cikin akwati? Ya rasa akwatuna nawa zai kawo mata sai akwatuna biyu? Maganganu kala-kala har ayi mata nuni da ƙawarta akwatuna shida aka kawo mata.

Iyaye sun kasa ganewa kowa da arzikinsa. Allah kaɗai yasan irin ƙoƙarin da yaje ya yi ayayin kawo kayan nan. A irin lokacin da aka kawo lefe, fatan alkhairi kawai da zama lafiya ake yi babu maganar ƙananan maganganu. Daga irin hakan ne sai aure ya lalace. Shi ango yana ganin an raina masa arziki, ita kuma amarya an zugata tana ganin tafi ƙarfin wannan lefen.

Dan haka ni gaskiya na bai wa lefe matsayin kowa ya tsaya a in da Allah ya ajiye shi. Iyaye su daure su kauda kai akan lefen da aka kawowa ‘ya’yansu. Bai zama dole a dinga nunawa duniya lefe ba, bare har ya zama abin ƙananan maganganu.

Domin naga wasu ma maza suke bai wa lefen akai gidan iyayen amarya, su kuma su kama kaya su rufe. Ya kamata a yanzu adaina nuna lefe, duk da al’ada ce ta malam Bahaushe. Amma idan muka yi la’akari da wannan al’adar na shi kansa lefen a yanzu an sauya abubuwa da yawa daga cikin al’adun an zamanantar da shi.

To ya kamata a yanzu agane kai ya waye, an wuce matsayin da dole sai an nunawa duniya irin lefen da aka kawo. Dan wani abu da yake yi mini ciwo, akan nunawa maƙota lefen nan, shi ne; sai wata ta ɗaga zani tana tave baki, tana cewa “Wannan ai ƙaramar atamfa ce. Wannan shaddar wanke kudinka ce.”

Idan ba a fada agaban uwar amaryar ba, ana fita za ayi ta maganganu har ya koma kunnen iyayen yarinya. Gaskiya su kansu suna taka rawa wajen ruguza aure. Domin akwai aurarrakin da bai yiwu ba, saboda kawai lefen da aka kawo bai yi masu ba, shi kuma ango ya dage bai da halin ƙaro wasu kayan. Allah sa mu dace.

Hajiya Saliha, idan mun yi kallo zuwa ga alfanun yin lefe, a tsakanin amarya da aka kawo wa lefe, da angon da ya kawo, zuwa danginsu, wa ya fi fa’idantuwa da lefen?

A nan Ina iya cewa kowanne ɓangare da irin fa’idar da suke samu da kayan lefe gaskiya.

Ta ɓangaren amarya an san mace ‘yar ƙwalisa ce, ba kuma za tayi adon da zai burge mijinta sosai ba sai da sutura da kayan kwalliya don haka yayin da aka yi sa’a amaryar ta yi dacen angon ya gwangwajeta da kayan lefe ba zata samu cikas wajen gyaran jikinta ba, musamman idan an ci karo da masu rauni na rashin wadata, ma’ana daman amaryar babu isassun sutura, irin haka an samu kyakkyawar rufin asiri don za ki ga wasu iyayen idan sun ga kayan lefe su kan ciccire wasu tsoffin tufafi na amarya a bai wa ƙanninta ko wasu cikin dangi tunda ita Allah yai mata sutura ta sami sabbi, a wani al’adar kuma har mahaifiyar amarya za a cirewa turmin atamfa a ba ta, wasu ana cire har biyu zuwa uku a bai wa ƙannin uwa ko na uba, yayinda a kan cire kamar su man shafawa da sabulai, gazar ko janbaki a bai wa ƙawayen amarya ko ƙanni, duk a zamani dauri nike magana ko da yake a yanzun ma akwai inda naga ana hakan.

Bugu da ƙari sau da dama ba kowanne namiji ne ke iya ɗinkawa Iyalinsa sutura akai-akai ba, daga sallah sai sallah, wani sai mace ta haihu, yayinda wasu mazan ko a shekarar ma ba zai ɗinkawa matarsa ko fallen zani ba, a nan wacce ta samu aka yi mata lefe ta iya adana abinta tana gyarawa ba zata yi rashin sutura nan da nan ba.

Bayan haka yanzun masu hannu da shuni idan zasu kai lefe sukan haɗa da akwatin uwar amarya da na uban ango har da jakar turamen dangin amaryar a wani ɓangaren.

A ɓangaren kuma tun farko ai kansa ya kyautatawa domin shi amaryar za ta sakawa kayan a jikinta ta yi masa kwalliya ya gani ya ji daɗi.

Sannan zai ɗauki dogon lokaci aljuhunsa bai yi kuka ba ta ɓangaren sutura ga Iyalinsa sai ya ji da kucin cefane da sauran lalurorin da Allah ya wajabta masa.

Shima idan an koma kan bidi’ar da wasu masu hannu da shunin suka ɓullo da shi cikin al’adar lefe yanzun, ango zai more yawan kayan garar da iyayen amaryar za su kai masa daidai gwargwadon abinda ya kai ko ma zarce hakan ga waɗanda suka ɗaurewa ƙarya abin zama.

Sis Fatima, ko za ki iya gaya mana naki ra’ayi kan yi wa mace lefe?

Ra’ayina akan yiwa mace lefe, ba laifi ba ne dan an yi lefe. Haka ba kuskure ba ne dan ba ayi lefe ba, tunda ba addini ba ne, al’ada ce mai ƙarfi.

Sai dai idan za ayi kamar yadda na faɗa a baya, a cire ƙarya, a cire ƙure ango. Idan kuma an yi a daure a karɓa da haƙuri, a lallaɓa akai yarinya ɗakinta.

Akwai mazaje da yawa waɗanda ba su da ƙarfin yin lefe mai tsada, shin idan babu ba za a karɓa da haƙuri ba?

Me zai sa hakan ya dinga zama tashin hankali? Idan al’adar za mu yi amfani da ita kamar yadda ake yawaita faɗa, ya kamata mu duba can baya. A yadda tarihi ya zo mana, bana jin ana fasa aure saboda lefe, ba na jin ana wulaƙanta lefe. Amma a wannan zamanin ya zama babbar al’adar da ake kokarin amayar da ita tamkar addini.

Ina nan akan baka ta lefe yana da kyau, muddin aka karɓe shi a yadda ya zo. Idan na ce aka karɓe shi a yadda ya zo ina nufin babu cin fuska. Babu wulaƙanta ango. Ita kuma amarya a zaunar da ita a nuna mata angonta ya yi ƙoƙari, ta gode masa idan ya zo.

Ana ƙarfafa mata gwiwa akan rayuwar aure ba lefe ba ne, idan ta shiga cikin gidansa zai kawo mata abin da ya fi lefe. A dai dinga tunatar da ita wannan lefen fa ba shi ba ne ƙarshen kyautatawarta da mijinta. A koya mata godewa mijinta idan ya kawo mata abu duk ƙanƙantarsa. A nuna mata illar renuwa.

Ina ganin idan ana yin hakan za a sami sauƙi sosai da fargaban da maza suke yi a wurin yin lefe. Za a sami cigaba da kuma tsoron yadda maza da yawa suke tsoron tunkarar aure saboda lefe. Wasu ma cewa suka yi in dai za a cire masu lefe, insha Allahu za su yi aure.

Ki fahimta! Ba fa lefen suke tsoro ba, abubuwan da za su zuba na daidai ƙarfinsu suke tsoron a kushe masu.

Dan haka ra’ayina ayi lefe amma kuma adaina ƙarya a lefe, adaina kushewa miji idan ya yi ƙoƙari wurin haɗa lefe.

Hajiya Saliha, me ya bambanta lefen da ake yi yanzu da kuma wanda aka yo can baya?

Abubuwa da dama sun bambanta lefen da ake yi yanzun da na dauri.

Misali : A da haɗa lefen kan zama tamkar wani abin bajinta ne ga ango da iyayensa har da dangi inda ake haɗa ɗan abinda Allah ya hore cikin mutunci ba tare da nuna ƙarya, almubazarranci da riya wajen haɗawar ko kaiwa ba.

Idan kuma za a kai lefen mutane ƙalilan da ba su wuce shidda ba daga dangin uwa da uban ango sukan kai inda can ɓangaren amarya za su karva cikin murna da farin ciki ba tare da raina duk abinda Allah ya hore ba, fatan kowa dai Allah ya sa albarka.

Kowanne abu za a bayar ko a saka cikin kayan lefen da ya danganci al’ada irinsu kuɗin tsintuwa ko kuɗin ɗinki da ake sakawa cikin jakar amarya gwargwadon ƙarfin ango da iyayensa ake yi musamman da ya kasance a da ɗin ma yawanci ba angon ke haɗa kayan shi kaɗai ba, iyaye ke haɗawa, ko ya yi wasu su da sauran dangi su yi sauran.

A da neman albarkar auren ya fi yawa a zukatan mutane saɓanin yanzun da al’amarin ya rikice, mutane suka gurvata al’adar lefe da ƙarya, almubazzaranci da kusan in ce rashin kunya ta ɓangaren amaryar da sauransu.

Abin nufi a nan shi ne, a wancan zamanin idan ana kai lefe akwati ɗaya, biyu zuwa uku ne yanzun daga shidda ne zuwa dozen.

Bayan kayan iyaye da na dangi da za a ware. Yawancin lefen yanzun wata amaryar ma ita ke haɗa abubuwan da take so da kanta ta hanyar faɗawa ango kalar tufafin da take so, yayin da wata kuɗin zata karɓa ta rinqa sayen kayan da kanta tana haɗa abinta. Ko a nemi masu kasuwancin haɗa kayan a tsadance a biya ta haɗa a dauka a kai.

Savanin da can da amarya ba ta san kalar kayan da za a saka mata ba, saboda ba tada wani zavi face abinda Allah ya hore aka dauko aka kawo mata saboda alkunya.

A dauri don za a kai lefe gidan iyayen amarya babu ruwansu da faɗuwar gaba da fargaban abinda za su dafa ko yawan kuɗin tukuicin da za su bayar ko ma abincin da za su ba jama’an da suka tara musamman domin a tarbo lefen kacokan.

A inda aka sha banban yanzun duk uwar da za a kawo lefen ɗiyarta ta shiga uku da faɗi tashin neman kuɗin yin toye-toye, sayen kaji, lemukkan sha kana da abincin da zata dafa na ‘yan kawo lefen zuwa waɗanda ta gayyato a zo a tarbo lefen ɗiyarta.

A wani wurin har da su kiɗan DJ, anko da raba kalandu, sannan a ɗauka a waya a na yaɗawa a kafafen sada zumunta don dai kawai a ga yawan tarin akwatunan da aka yiwa wata.

Wasu lefen da ake haɗawa a wannan zamani kai ka ce amaryar ba za ta ƙara sanya wasu kayan ba sai su saboda yawansu.

Bashi ya shigo cikin haɗa kayan lefen yanzun dalilin yawancin mazan ba su tsayawa matsayin abinda Allah ya hore musu wanda yawanci tunanin za a raina abinda suka yi ko kuma su ɗinne a karan kansu ke son nuna ƙarya da na isan ban isa ba kan jawo musu tsunduma cikin masifar bashi.

Yawanci iyaye sun fi ƙaunar su ga ko su ji ana labari tare da yayata yawan akwatunan lefen da aka kawo wa ‘Ya’yansu ba tare da tunanin hakan ba zai kawo ingantacciyar zamantakewar ba.

Za mu ci gaba a sati mai zuwa.