Makarantun tsangaya (Almajirci) gyars kaɗan suke buƙata ba haramta su ba

Daga ABUBAKAR SANI

Karatun tsangaya wani irin karatu ne wanda ake yi a makaratun koyar da addinin musulunci a ƙasar Hausa shekaru da dama da suka wuce. Karatun ana yin sa ne ta hanyar yin rubutu a allo da kuma alƙalami. Ma fi yawan waɗanda suke yin wannan karatun su ne suke ciyar da kansu ta hanyar yin bara domin su samu abinci. Masu yin wannnan karatun yawancin su karatun Alƙur’ani kaɗai suke yi babu ruwansu da karatun boko. Haka kuma ma fi yawancin su ba su cika yin sana’a ba sai dai bara, wanda ake kira da almajiranci.

A ƙoƙarinmu na samar da gamsasshen bayani ga al’umma mun gutsuro wasu bayanai daga rubutun Shugaban Sashen addini na jami’ar Bayero, Farfesa Ahmad Murtala. Allah ya ƙara masa hasken makaranta.

Makarantar allo suna ne mai faɗi da ya haɗa da waɗanda ake yi a lunguna cikin birane, waɗanda wani lokaci ɗalibai daga ƙauyuka za su zo su haɗu da ɗaliban cikin garin zalla, masu zuwa su koma gidajensu. Sannan kuma ya haɗa da makarantun tsangaya da ɗaliban za ,su bar gidajensu su tafi wajen gari ko wasu ƙauyuka da garuruwa don neman Ƙur’ani. Waɗannan duka, sunansu makarantun allo.

Manufarmu da waɗannan bayanai, ita ce: a ba da shimfi]ar da za a san yadda tsarin karatun allon ya taso da irin abubuwan da ake aiwatarwa a cikinsa. Abin la’akari dai shi, shi ne ba wani sabon abu ba ne mutanen Ƙasar Hausa suka ƙirƙiro, tsari ne na koyarwa tuntuni.

Ko da wasu makarantun ko ɗaiɗaikun mutane sun yi wasu abububwa na rashin kirki ko sun zarce gona-da-iri a aikata wasu abubuwan za a zarge su ne su kaɗai amma ba tsarin bakidaya za a tsangwama ba. Domin miliyoyin mutane sun bi ta kansa sun zamo malamai, sun amfanar, wasu kuma suna ta amfanar da al’umma har gobe.

Wannan faɗakarwa za ta yi fa’ida ga mutanen da ba su yi ko sun ratsa ta cikin irin wannan karatu ba. Ko kuma ba su tashi a wuraren da ake yin sa kwata-kwata ba. Fatan mu ya zamo fitila ga waɗanda ake zugo su daga ƙungiyoyin Turawa na Duniya don su ƙarasa abinda ‘yan mulkin mallaka suka fara. Haka nan, muna fatan ya ganar da ruɗaɗɗun ‘yan kallo.

Muhimmancin karatun allo:

1-Muhimmancin Fara Rayuwa Da Karatun Allo: Imamu Abdurrahman bn Khaldun ya faɗi muhimmanci koyan karatun Ƙur’ani tun daga yarinta. A cikin bayanin nasa yana cewa: “Koyar da yara Ƙur’ani Babbar alama ce ta kafuwar addinin Musulunci. Duka Musulmi sun yi riko da wannan hanya, sun ci gaba da tafiya a kanta a garuruwansu. Saboda imani yana rigaye zuwa cikin zukata ya zauna. Haka nan kuma aƙidun Musulunci da suka tabbata da ayoyin Ƙur’ani da wasu hadisai duk suna tabbatuwa a zukatan. A kan Ƙur’ani asalin tsarin koyarwa, wanda ya nan wasu kuma ake samun ƙwarewa daban-daban suke tabbatuwa. Dalilin haka kuwa shi ne, koyar da yaro tun yarintarsa ya fi zama daram. Shi ne kuma asalin abinsa zai zo daga baya. Saboda abinda ya yi saurin shiga zukata yana zamowa tamkar tubali ga duk ƙwarewar da za ta zo daga baya. Bisa yadda ya ginu duk sauran abubuwan da za su zo, su ma haka za su kasance. Akwai hanyoyi iri-iri da malamai suke bi wajen koyar da yara. Saɓanin ya biyo bayan irin abinda ake son tsarin koyarwar zai sama wa yaran na ƙwarewa”.-(Mukaddimatu Ibnu Khaldun: sh/537-538).

2-Lokacin Karatu: Ana yin karatu tun asabar har alhamis. Zai sa musu lokutan wanke alluna da yin “sabon rubutu”, da lokutan “gyara alluna” da lokutan “ƙarin karatun”, da lokutan “ba da hadda”, da sauransu. Lallai a fayyace wadannan lokutan a gudanar da su a kan tsarin da bai karye ba.-(Madkhalna Ibnul Haj).

Ana yin karatu tun asabar har yammacin Laraba. A wasu wuraren har safiya alhamis. Wasu su kai shi har yammacin alhamis. A cikin waɗannan Kwanaki, malami zai sa musu lokutan da zai dinga gyara allunan yaran da lokutan da zai ba su dama su wanke allunan bayan sun iya ko sun haddace. Haka nan zai fitar da lokutan ƙarin karatun da lokacin sauraron hadda.

Zai iya sauraronsu a ɗaiɗaiku ko mutum bi-biyu ko fiye da haka yadda abinda zai zo da sauƙi kuma ya biya bukatar da ake so. Idan dai ba iyaye ne suka nuna suna son yaronsu ya yi karatun zuƙu ba, to wajibi malami ne ya tabbatar da cewa yaro ya haddace sura kafin ya shiga wata –(Adabul Mu’allimin na Ibnu Suhnun: sh/109 da 115). A yawancin makarantu, yaro yana yin rubutu sau biyu ne a sati. Ya rubuta Asabar misali, ya wanke litini da rana. Sannan ya rubuta wani. Shi ma zai wanke shi a ranar Laraba. Ranakun Alhamis da Juma’a kuma, zai samu lokacin da zai dandaƙi abinda ya koya a cikin sati, ya yi takara da tilawa yadda ya kamata.

A ranaku kuma, kamar yadda aka faɗa a baya, ana fara karatun tun ranar Asabar har zuwa yammacin Laraba. Wasu kuma suna yi har zuwa safiyar Alhamis. Wasu su kai shi har yammacin Alhamis. Wannan dangane da makarantun cikin gari kenan, wadanda yaran cikin gari suke halarta.

A yawancin lokaci a irin wadannan makarantu ba yaran cikin garin ne kadai suke zuwansu ba, akwai wasu yaran da suka zo daga ƙauyuka da wasu biranan suna kwana a shaguna da soraye da mutanen unguwa suka ba su su zauna. Ko kuma in malamin yana da ƙarfi, ya samar da gidan da za su ƙika kwana. Irin waɗannna ɗalibai su suna da nasu tsarin na karatun ƙari a kan na sauran ɗaliban cikin gari. Su ɗaukar tsarin tsangayoyin da ake yi a wajen gari.

A makarantu da yawa suna tashi “Karatun-Dare”, galiban bayan sallar isha, su daɗa tisa karatunsu zuwa kamar awa biyu ko fiye da haka kaɗan. Daga nan sai su kwanta kuma sai gobe su tashi su ci gaba bayan asuba har zuwa hantsi. Wannan bai hana masu ƙwazo su tashi da dare su yi ta kwami ba!

Makarantun tsangaya sun ba da gudunmuwa sosai wajen cigaba da kuma yaɗa addinin musulunci musamman a Arewacin Nigeria da kuma wasu ƙasashe a yanmacin Afirka.
Bayan cigaba ta ɓangaren yaɗa addinin musulunci, makarantun sun taimaka sosai wajen samar da zaman lafiya da kuma tausayi da ƙaunar juna, saboda mai tausayi ne kaɗai zai iya ba wa almajiri abinci sadaka.

Canjin lokaci da kuma zamani da aka samu, ya sa karatun tsangaya ya lalace saboda salon yadda ake koyar da shi a zamanin da muke ciki, ya saɓa wa walwalwa da jin daɗin rayuwar ɗan adam.

Dalilan da ya sa na ce salon koyar da shi ya saɓa walwala da jin da ɗin rayuwar ɗan adam su ne:
1- Babu wani addini ko ƙabila da ya halarta yin barace-barace haka kuma gwamnati ma ba ta yarda da yin bara ba. A zamamin da can, zai wuya ka ga almajiri ya wuni bai samu abinci ba, amma kuma yanzu zamanin da muke ciki wani ma yana kwana bai ci abincin ba kuma babu mai damuwa da ci ko shan sa.

2- Babu wani addini ko ƙabilar da ta yarda ka bar ɗanka da bai wuce shekara goma sha takwas ba ya ɗauki ɗawainiyar kansa. Amma yanzu matsalar da muke fuskanta a karatun almajiranci, sai ka ga an kai yaron da bai wuce shekara goma ba karatu can wata jaha, kuma shi ne zai ciyar da kansa ya tufatar da kansa Kai tsaye zan iya cewa haka cin zarafin ƙananan yara ne.

3- Babu wani addini ko ƙabila da ta yarda ka zauna babu sana’a ko kasuwanci. Amma matsalar ita ce mafiya yawan almajirai bara ita ce babbar sana’ar su, wanda hakan ya saɓa wa dokar dukkan ƙabilu, addinai, da kuma gwamnati.

4- Da yawan lokaci idan almajiri ba shi da lafiya malamansu ba su cika kai su asibiti ba sai dai su bar su a gida. Kuma a haka almajiran su ne ke ciyar da kansu. A dalilin haka almajirai da dama sun mutu wasu kuma sun shiga mawuyacin hali.

Wasu gwamnatoci da suka shu]e sun yi ƙoƙari sosai wajen gina makarantun kwana na almajirai wanda ake ba wa almajirai cikakkiyar kulawa kamar yadda ake ba wa makarantun kwana na gwamnati. Wasu gwamnatocin kuma suna yaƙin karatun ne kuna sun haramta shi a jahohinsu.

Ƙungiyoyin sa kai musamman a kafafen sada zumuntan suna yaƙi sosai da salon karatun almajiranci na wannan zamanin. Wasu suna da burin a haramta shi gabaɗaya wasu kuma suna da burin a yi masa gyaran fuska ne a saita shi ya tafi dai-da da zamani, yadda kowa zai samu rayuwa mai inganci.

Amma ni a nawan tunanin, waɗannan ƙungiyoyin ba za su taɓa kawo sauyi a harkar karatun almajiranci ba, saboda salon da suka ɗauka ba zai iya canza komai ba. Kaɗan daga cikin dalilan da suka sa na faɗi haka su ne:

1- Ma fi yawan su a shafukan sada zumunta da’awarsu take ƙarewa. Su kuma malamai da iyayen yaran wasu ma ko wayar andiroyi (android) ba su taɓa riƙewa ba, balle su shiga shafukan yanar gizo su gani.

2- Ba su da ladabin magana da kuma hikimar ƙulla zance. Mafiya yawan masu yin wannan da’awar sun fiye yin magana gatsa-gatsa. Za ka ga mutum yana so ya wayar wa da mutane da kai ne amma kuma yana zagin mutanen to dan Allah ta yaya za su saurare shi? Misali sai ka ji mutum na cewa ” Ai jahilci ne da rashin imani zai sa mutum ya kai yaronsa karatun Allo.” To dan Allah da wannan maganar ta yaya kake tunan iyaye ko malaman yaran za su tsaya su saurare ka har su fahimci abunda kake nufi?

3- Mafiya yawan masu yin wannan da’awar suna kira ne ga gwamnati da ta kashe abun gaba ɗaya. kaɗan daga cikinsu ne suke kira a yi masa gyara. To gwamnatin da ta kasa gyara makarantunta na zamani ita ce kuke su ta waigo ta kalli tsangaya?
Kuma a duk lokacin da gwamnati ta yi wani yunƙuri a kan wannan maganar. Sai dai ta ce za ta yi amfani da ƙarfi wajen haramta karatun tsangayar ba wai ta gyara shi ba. Kaɗan daga cikin gwamnatoci ne suke kokarin kawo gyara.

Idan kuna son kawo gyara a wannan harkar, to ga kaɗan daga cikin hanyoyin da ya kamata a bi:
1- Masu yin wannan da’awar su samu ladabin magana da kuma hikimar ƙulla zance. Su dinga taren mutane da tausasan kalamai wanda zai sa a fahimci manufarsu.

2- Kada su sake su ce za su tari iyaye da malaman tsangaya kai tsaye saboda ba dole ne su saurare su ba. Su yi ƙoƙari su samu masu sarautar gargajiya da sauran manyan masu kuɗi da yan bokon garin da suke son su yi da’awarsu, su zauna da su su yi musu bayani sosai su fahimta. Waɗannan mutanen su ne za su tattaro malamai da iyayen yaran kuma dole su zo su saurari saƙon da kuka zo da shi.

4- Bayan sun tara iyaye da malaman yaran, kada su sake su ce za su kawo masu illar almajiraci ko bara. Kaɗan abunda za su faɗa musu shi ne;
Mahimmancin karatun Alƙur’ani da kuma irin rawar da makarantun tsangayu suka taka wajen bunƙasa addinin musulunci
Mahimmancin karatun boko da kuma Nasarori da ‘yanboko da suka yi karatun allo suka samu a rayuwa.

Mahimmancin sana’a da kuma rawar da take takawa wajen kawo gyara a rayuwar ɗan adam musamman matashi.

Daga ƙarshe sai su fa]a wa malaman cewa ya kamata a bayan yaran sun yi karatunsu na allo, to yakamata su je makarantar boko domin inganta rayuwar a wannan zamanin. Sannan idan sun taso daga boko su je wajen sana’a inda za su samu kuɗin kashewa har da ku]in Laraba wanda za su yi wa malamansu hidima da shi.

Makarantar boko akwai na gwamnati wanda ba a biyan ko sisi. Masu yin wannan da’awar su yi alkawarin kula da yaran kuma su cika wannan alkawarin su. Kin ga zuwa suna duba su a kai-a kai.

Na tabbata insha Allah idan aka bi waɗannan hanyoyin za a iya yin maganin matsalar, amma da’awa a shafukan sada zumunta ba zai taɓa magance ta ba. Nan gaba zan ƙara yin sabon rubutu a kan wasu hanyoyi masu sauƙi da za a bi domin magance matsalar.

Abubakar sani (Kwamared Ɗan Bahaushe) ya rubuto ne daga Jami’ar Ahmadu Bello, Kaduna, Zaria.