Malaman Jami’ar Kaduna sun janye yajin aiki bayan barazanar korarsu da El-Rufa’i ya yi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Bayan rantsuwa da Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya yi cewa sai ya fatattaki duk wani malamin Jami’ar Jihar Kaduna, KASU, da ya cigaba da yajin aiki, Malamai sun dawo aiki gadan-gadan a ranar Litinin.

Rahotanni da suka iske Manhaja sun nuna yadda ɗalibai suka yi tururuwa zuwa jami’ar domin ci gaba da karatu.

Sai dai kuma ba karatu aka yi ba a wannan rana, inda ɗaliban sun ci gaba da jarabawa ce wacce suna tsaka da zana wa aka tafi yajin aikin.

Ɗalibai sun garzaya ɗakunan karatu duk sun zauna domin fara rubuta jarabawa.

Idan ba a manta ba a cikin makon jiya gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya yi rantsuwar cewa duk malamin da ya shiga yajin aikin malaman jami’o’i zai fuskanci hukuncin gwamnati.

”Na rantse duk malamin da ya shiga yajin aiki zan kore shi aiki. Domin jami’ar gwamnatin jiha ce KASU ba ta Gwamnatin Tarayya ba. Mu ne muke biyansu albashi saboda haka dole su koma aiki. Wanda kuma ya ƙi zai gani a kwanonsa.

”Sannan kuma za mu duba duk wanda ya karɓi albashin mu kuma ya yi yajin aiki a baya zai biya mu idan muka gano haka.

Har yanzu malaman jami’o’i na cigaba da yajin aikin a faɗin ƙasar nan. Sun fara yajin aiki tun daga watan Fabrairu har yanzu.

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya umarci Ministan Ilimi da ya saka baki sannan ya gaggauta ganin an samu maslaha tsakanin malaman da gwamnatin cikin gaggawa domin ɗalibai su koma karatu.

Da yawa daga cikin iyaye sun fara cire ‘ya’yansu daga jami’o’in gwamnati suna maida su jami’oi masu zaman kansu.