NDLEA ta rufe gidan abinci bisa zargin sayar da kayan maye a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi a Nijeriya ta NDLEA ta rufe wani gidan abinci da take zargin ana sayar da kayan maye tare da kama kusan mutum 51 a Kano.

BBC Hausa ta rawaito cewa hukumar ta NDLEA ta ce ta kama mutanen ne bayan samun ƙorafi daga mazauna unguwar da gidan abincin yake a titin Lamido Crescent da ke cikin birnin na Kano, saboda yadda matsalar ke neman gurɓata tarbiyyar ‘ya’yansu.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wata kotun gwamnatin tarayya da ke Kano ta aike da wani mai sayar da magungunan jabu zuwa gidan yari na tsawon shekaru uku, tare da biyan tarar Naira 200,000.

Can ma a birnin Legas da ke Kudancin ƙasar NDLEA ta kama ƙwayar Tramadol sama da miliyan biyu da dubu ɗari bakwai, da aka yi yunƙurin fita da ita ƙasashen waje daga tashar ruwan Apapa.

NDLEA ta ce ƙwayar na ɗauke ne a cikin katan-katan 55, da suka haɗa da nau’ukan Tapentadol da kuma Carisoprodol na Tramadol, da kuɗinsu ya kai Naira miliyan ɗaya da dubu ɗari uku da saba’in da biyar.