‘Yan fashin daji na ta kwararowa jiha ta, Gwamnan Nasarawa ya koka

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana damuwa game da yadda gungun ‘yan fashin daji ke tururuwa zuwa jiharsa bayan koro su daga maƙwabtan jihohi.

BBC ta rawaito cewa, Gwamna ya ce jami’an tsaro sun lura da ƙaruwar ‘yan bindiga a Ƙaramar Hukumar Karu, wadda ke da nisan ƙasa da kilomita 30 daga Abuja babban birnin ƙasar.

“Mun lura da tarin ‘yan fashin nan da aka koro daga jihohin Kaduna da Katsina da Neja da Kebbi musamman a yankunan Rugan Juli da Rugan Madaki da ke Ƙaramar Hukumar Karu,” a cewar gwamnan yayin taron manema labarai ranar Asabar.

“Kazalika, mun ga wasu daga cikinsu a ƙananan hukumomin Wamba da Toto.”

Haka nan gwamnan ya ce sun yi nasarar kama wasu daga cikin fursunonin da suka tsere daga gidan yari na Kuje a Abuja bayan mayaƙan Boko Haram sun fasa shi a watan Yuni.

Wasu mazauna yankunan da Gwamna Sule yake magana sun faxa wa BBC Hausa cewa sun shaida ƙaruwar satar mutane a yankunan nasu.