Masarautar Uke ta naɗa Kola a matsayin Kuyambana Babba

Daga BASHIR ISAH

A matsayin wani mataki na ci gaba da ƙarfafa wa matasa wajen yi wa al’umma hidima, Masrautar Uke da ke yankin ƙaramar hukumar Karu a jihar Nasarawa, ta naɗa Mr Slomon Aliyu Kola (FCIA) a matsayin Kuyambana Babba na masarautar.

Naɗin Kuyanmbana Babba ya gudana ne a fadar Maimartaba Sarkin Uke, Alh. Dr. Ahmed Abdullahi Hassan (KOBA) (Yakanajen Uke) a ranar Larabar da ta gabata.

Da yake jawabi yayin naɗin, Sarkin Uke, Alh. Dr. Ahmed Abdullahi Hassan, ya ce masarautarsa a shirye take ta tafi tare da duk wani mai son cigaban al’umma ba tare da la’akari da bambancin addini ko ƙabila, ko ɓangare ba.

Kana ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga matasan Nijeriya da su daina barin ana amfani da su wajen cim ma manufofin siyasa da duk wani al’amari da ya saɓa wa dokar ƙasa.

Da yake magana da waikilinmu jim kaɗan bayan naɗin nasa, Mr Kola (Kuyambana Babba na Uke), ya nuna godiyarsa dangane da karamcin da Masrautar Uke ta nuna masa. Tare da cewa, da yardar Allah zai yi amfani da wannan dama wajen ci gaba da yi wa al’umma hidima kamar yadda ya saba.

Mr Kola ya yi kira ga al’ummar Masarautar Uke da su ci gaba da bai wa Sarkin Uke da muƙarrabansa haɗin kan da ya dace domin ba su damar sauke nauyin da ya rataya a kansu yadda ya kamata.