Brisbane ta samu gurbin ɗaukar nauyin Wasannin Olympic na 2032

Spread the love

Daga UMAR M. GOMBE

Kwamitin Shirya Wasannin Olympic na Ƙasa da Ƙasa ya bayyana birnin Brisbane na ƙasar Australia a matsayin birnin da zai ɗauki nauyin gudanar da Wasannin Olympic na 2032.

Da wannan sasarar da Brisbane ya samu, ya sanya Australia ta zama ƙasa ta biyu a duniya bayan ƙasar Amurka da suka samu damar ɗaukar nauyin gudanar da Wasannin Olympic fiye da sau biyu a birane daban-daban.

Da farko, Australia ta soma ɗaukar nauyin Olympic ne a Melbourne a 1956, sannan Sydney a 2000, sai kuma na ukun kenan ake sa ran gudanarwa a Brisbane ya zuwa 2032.

Ita kuwa ƙasar Amurka, ta soma ɗaukar nauyin Olympic ne a 1904 a St. Louis, sannan a Los Angeles 1984 da kuma 1996 a Atlanta, sai L.A. a 2028.

Kwamitin shirye-shirye na Olympic ɗin Brisbane ya ce ana sa ran tattalin arzikin yankin ya samu amfani na kimanin Dala bilyan $17 albarkacin gasar Olympic ɗin da za a gudanar.

Firam Minista Australia, Scott Morrison, ya ce gwamnatin ƙasar a shirye take ta ba da cikakken goyon bayanta domin ganin an gudanar da wasannin cikin nasara.

By Editor