Buhari ya tabbatar da sauke Hadiza Bala-Usman a matsayin shugabar NPA

Daga AMINA YUSUF ALI

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya tabbatar da sauke Hajiya Hadiza Bala-Usman a matsayin Shugabar Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NPA).

Buhari ya tabbatar da hakan ne a ranar 12 ga Yuli cikin wata takardar kotu a Legas sakamakon ƙararar da babban jami”i na kamfanin Maritime Media Limited, Asu Beks, ya shigar a kansa da kuma wasu mutum biyu.

Ƙarar mai ɗauke da lamba FHC/L/CS/485/2021, wanda ya shigar da ita ya ƙalubalanci ikon da Buhari ke da shi na kafa hukumar gudanarwa na NPA tare da ɗora babban darakta ba a bisa dokar NPA ba.

Kazalika, cikin ƙarar an ƙalubalanci Shugaba Buhari da sake naɗa Hadiza Bala-Usman kan muƙaminta watanni shida kafin ƙarewar wa’adinta.

Jami’a Agan Tabitha daga Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya da ke Anuja, ita ce ta sanya wa takardar kotun hannu a madadin lauyan Buhari.

Buhari ya ce da jimawa aka sauke Hadiza Bala-Usman daga matsayin da aka yi zargin an sake naɗa ta wanda aka gabatar wa kotu don ta yi shari’a a kansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *