Chaina ta soma aikin shimfiɗa bututun mai daga Nijar zuwa Benin

Daga WAKILINMU

Da alama Nijeriya ta rasa damar samun kwangilar bilyoyin Dala na aikin shimfiɗa bututun mai da ƙasar Chaina ta ɗauri aniyar aiwatarwa bayan da masu zuba jari na Chaina suka sauya ra’ayin karkatar da akalar kwangilar zuwa maƙwabciyar Nijeriya, wato Nijar.

Bayanai sun nuna Kamfanin China Petroleum Pipeline Engineering Co. Ltd. (CPP) wanda ɓangare ne na Kamfanin Fetur na Ƙasar Chaina (CNPC), ya soma aikin shimfiɗa bututun mai wanda za a riƙa tura ɗanyen mai daga Tarayyar Nijar zuwa matattarar mai da ke Seme-Krake a ƙasar Benin.

Bayanai sun ce aikin wanda ya samu tsaiko na wasu watanni sakamakon barazanar annobar korona, yana da tsayin kilomita 1,980, ana sa rana bayan kammalawa ya zuwa 2024 zai taimaka wa Nijar wajen bunƙasa yawan man da take samarwa daga ganga 20,000 duk rana zuwa ganga 120,000.

Aikin shimfiɗa bututun wanda aka yi wa laƙabi da Niger-Benin Export Pipeline (NBEP), an ce zai laƙume kuɗi har Dala bilyan $7. Kuma aikin zai tashi ne daga yankin Agadem na ƙasar Nijar zuwa Tarayyar Benin.

Alamu masu ƙarfi sun nuna cewa, Nijeriya ta rasa wannan dama mai gwaɓin gaske wadda albarkacinta za ta samu maƙudan Daloli wanda hakan ka iya ƙara wa tattalin arzikinta tagomashi.

Binciken Manhaja ya gano cewa, da farko an shirya gudanar da aikin shimfiɗa bututun ne tare da gwamnatin Nijeriya inda za a jera bututundaga Nijar zuwa babbar tashar jirgin ruwa da ke bodar Seme a ƙasar Benini, amma daga bisani sai shawarar ta canza.

A cewar wasu da ke da masaniya game da aikin, tun a 2006 kamfanin man na ƙasar Chaina (CNPC) yake ta ƙoƙarin ganin yadda zai gina hanyar da zai samu yana fitar da ɗanye mai daga Nijar zuwa gaɓar tekun Benin.

Haka nan, sun yi ra’ayin cewa maiyiwuwa ƙorafin da wasu ‘yan ƙasa suka yi ya sa Nijeriya ta nuna ba ta da buƙatar aikin da ƙasar Chaina wanda hakan ya sa aka maida aikin ga Nijar.